✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda magidanci ya mutu garin ceton tunkiya

Wani magidanci mai shekara 55 ya gamu da ajalinsa a kokarinsa na ceto tunkiyarsa da ta fada rijiya. Lamarin da ya faru a kauyen Sha’iskawa…

Wani magidanci mai shekara 55 ya gamu da ajalinsa a kokarinsa na ceto tunkiyarsa da ta fada rijiya.

Lamarin da ya faru a kauyen Sha’iskawa a Karamar Hukumar Dambatta ta Jihar Kano ya jefa al’ummar yankin cikin zullumi.

Marigayin mai suna Abdul-Hamid Muhammad ya yi kokarin ceto tunkiyar da ta fada rijiyar ne bayan da ya shiga cikin rijiyar ya fita daga hanyyacinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Sa’idu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an yi kokarin ceto rayuwar mamacin, aka kai shi Babban  Asibitin garin Dambatta, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

“A ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2020 da misalin karfe 4:37 na yamma wata mace mai suna Ummu Muhammad da ke kauyen na Sha’iskawa ta sanar mana da faruwar lamarin ta wayar salula.

“Jami’anmu sun isa wajen inda suka iske mutumin mai suna Abdul-Hamid Muhammad wanda ya fada rijiya

“Bayan mun fito da shi daga rijiyar mun garzaya da shi Babban Asibitin garin Dambatta inda likitoci suka tabbatar ya rasu”, inji shi.