✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya birkice wa banki kan bacewar N1.5m daga asusunsa

Mutumin ya dare kan dakalin cikin bankin sannan ya kwabe rigarsa ya yi zaman ’yan bori ya ci gaba da tada hankalin ma'aikatan bankin.

Wani magidanci ya tara ’yan kallo a cikin banki bayan da Naira miliyan daya da dubu dari biyar da ke asusunsa ajiyarsa ta yi batan-dabo.

Bidiyon da aka yada a kafafen sadarwa na zamani ya nuna mutumin ya dare kan dakalin cikin bankin sannan ya kwabe rigarsa ya yi zaman ’yan bori ya ci gaba da tada hankalin ma’aikatan bankin.

Bayanai sun ce, magidanci ya tafi bankin ne domin bincikar dalilin da ya sa aka kwashe masa kudi ba tare da saninsa ba.

An ce mutumin ya yanke shawarar aikata haka ne bayan da ya rasa samun gamsasshen bayani kan bacewar da kudaden nasa suka yi daga asusun nasa.

Wannan ala’amari na ci gaba da daukar hankalin mutane, musamman a kafafen sadarwa na zamani, inda wasunsu ke zargin bankuna da kwashe wa kwastomominsu kudi ba tare da dalili ba.