Idan yau dukkan azzaluman shugabannin da muke da su a ko’ina cikin kasar nan (na cikin gida ko addini ko gargajiya ko hukuma ko na sana’a) za su mutu ko su kau daga doron kasa, ba wani sauki za a samu ba, domin Allah Ya riga Ya halicci wani azzalumin da ke jiran hayewa kan gadon mulkin domin ya ci gaba da tursasa wa al’umma a kowane irin fasali ko tsari. Kila ma in ba a yi hankali ba, wadanda za su hau su kasance sun fi wadanda suka wuce iya zalunci da tursasawa, domin al’umma na tafiya ne da irin shugabannin da ta samar wa kanta, ba wai daga wata kasa za a shigo da su ba!
Ke nan matsalar kasar nan ba ta shugabanni ba ce kadai, matsala ce ta kowa da kowa! Don haka sai talakawa sun gyara tsakaninsu sannan za su samu adalin shugaba ko shugabanni.
Me wannan yake kara tabbatar mana? Shi ne ita rayuwa irin ta shugabanci da ingantancen tsarin zamantakewa tsakanin shugaba da talakawa ko wadanda ake mulka tamkar babbar gona ce wadda ke tattare da taki ga kuma iri da za a shuka domin a samu yabanya mai kyau. Bisa tsari da tunanin kwarai ba yadda gonar da aka zuba mata taki, aka kuma shuka gyada a farka a lokacin girbi a samu doya ko dankali ko shinkafa a cikinta. Wato dai abin nan ne da Hausawa ke cewa abin da ka shuka shi ne za ka girba.
Idan muka yi amfani da wannan tunani za mu ga cewa duk tsawon da aka yi ana mulkar al’ummar kasar nan, cikin jin dadi ko wahala, da sonsu, ko da kinsu, ba abin da yake nunawa face halayyar da al’ummar da ta samu kanta ne ke kara bayyana. Ke nan ba wani ko wadansu ba ne ke zuwa daga wajen al’ummar domin gabatar da kansu a matsayin kyawawan shugabanni ko kuma lalatattu. In da kila za a iya cewa ana samun wabai shi ne wajen da baki ne suka mulki al’ummar ba ’yan kasa ba, a nan muna iya bayar da misali da mulkin mallakar al’umma da ya wakana a tsawon tarihi, to amma shi ma bai rasa nasaba da halayyar al’ummar da aka mulka suke ciki.
Saboda haka idan muka koma cikin tarihi, muka yi nazari da kyau za mu fahimci cewa ai tun ran gini, ran zane, kuma ita wannan rayuwar da muke ciki a halin yanzu ai can da ba haka take ba. Kafin wannan yanayin kunci da rashin jin dadin rayuwa da muka samu kanmu ciki, ai iyaye da kakanni na gaya wa na baya cewa, rayuwar da din ta fi armashi da annashuwa, domin kuwa da talakawa da shugabbanin rawa daya suke takawa, ba irin yanzu ba da rawar daban, masu takawa su ma daban, balle kuma uwa-uba kidan da ke tafe da sauti da rauji, mabambanta.
Dangane da haka in har muna son mu fice cikin kunci sai mun sake duba halin da muke ciki da kuma halayyar mabambantan shugabannin da muka yi a baya da wadanda muke da su a halin yanzu.
Mun dai sha fada an ci kwakwa zamanin shugabannin baya, tun daga Shagari zuwa Buhari zuwa Babangida da Abacha da Abdulsalam da Obasanjo da ’Yar’aduwa da Jonathan, yanzu kuma ga Buhari. Ba irin kuwwa da ihun da ba mu sha yi ba cewa shugabannin namu mugaye ne, sun tasa mu gaba, sai gallaza mana suke, amma mun manta cewa wadannan shugabanni daga cikinmu suka fito, iyayenmu ne ko ’ya’yanmu ko ’yan uwanmu ne, muna ci da sha da tarayya da su, idan sun gallaza mana to da alama, mu ma muna gallaza wa wadansu ne a cikin al’ummar. Saboda haka ba a taba samun na kwarai daga cikin lalatattu.
Kila samun amsar tambayar da muka yi tunda farko zai zama da sauki in mun fahimci cewa ba za mu fita daga cikin wannan kunci ba sai mun gyara, mun canja, mun kuma sawwaka wa juna a zamantakewar yau da kullum! Ta yaya?
Kai mai sayar da tumatir ko kayan marmari ko ke mai sayar da man gyada ko kuli-kuli da daddawa, me kuke yi wajen kyautatawa da inganta rayuwar sauran al’umma da kuke hulda da su?
Kai malamin makarantar allo ko na boko ko masinja ko kansila ko ciyaman ko sakatare ko wani dan kwangila ko dan siyasa me kuka yi na tagaza wa kasa da al’umma daga cikin irin halin ni-’ya-su da ake ciki? Ta yaya za mu nemi fita cikin kunci alhali kuwa muna cikin kuntatawa da lalata rayuwar sauran al’umma?
Ba za mu taba samun sauki ba sai mun saukaka! Ba za mu taba fita daga cikin kunci ba, sai mun fitar da sauran a’umma daga nasu kuncin. In mun kwana muna kira a samar mana da canji a ciki kasar nan, ba za mu taba ganin canjin nan ba, sai mu mun canja, ta kowace irin fuska. Domin kuwa wadanda muke son su fito domin kawo canjin ai daga cikinmu ne za su fito, ba daga wata uwa duniya ba.
Sauyi ko canji ko ci gaba mai amfani za su samu wurin jama’a ne lokacin da muka aza harsashin canjin daga cikin gidajenmu da unguwanninmu da kauyukanmu da garuruwanmu da biranenmu da ma dukkan rayuwarmu ta yau da kullum. Ba yadda mutum zai auri kunci, ya haifi kunci, sannan ya ce kunci ba zai zame masa riga da wandon rayuwa ba!
Idan kunne ya ji, Hausawa na cewa jiki ya tsira!