✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Mafi yawan daliban firamare a Arewa jahilai ne”

Wani kwararre a fannin ilimi, Mista bictor Ogbonnaya ya ce bincike ya nuna cewa fiye da kashi biyu bisa uku na daliban da suka kammala…

Wani kwararre a fannin ilimi, Mista bictor Ogbonnaya ya ce bincike ya nuna cewa fiye da kashi biyu bisa uku na daliban da suka kammala makarantun firamaren a yankin Arewacin Najeriya jahilai ne.
Mista Ogbonnaya wanda shi ne Manajan Gudanarwa na kungiyar Horar da dalibai (Skills Outside School Foundation), ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya a Abuja.
Ya ce: “Ingancin ilimi yana fuskantar barazana a yankin Arewa. Harkar ilimin ta tabarbare har ta kai ga a yanzu bincike ya nuna cewa fiye da kashi biyu bisa uku na daliban da suka kammala aji shida na firamare suna ci gaba da kasancewa jahilai.”
Ya bayyana cewa adadin ya ninka a yankin Arewa maso Gabas inda adadin ya kai kashi 72 bisa dari.
Kamar yadda ya ce, kashi 29 bisa dari na adadin daliban ba su iya bayar da amsar lissafi mai sauki idan aka kwatanta da takwarorinsu na yankin Kudu maso Yamma.
Ya bayyana cewa rashin tsararriyar manhajar ilimi da karancin gine-gine da kayan karatu suna daga cikin matsalolin da suke haddasa rashin ingancin ilimi a yankin.
Ya ce karancin malamai da yawan dalibai da kuma rashin tsari na daga cikin abubuwan da suke jawo sakamako marar kyau ga daliban.
Ya bayyana cewa yawan dalibai ya ninka yawan da dokar yawan dalibai ta kasa ta tanada a yankin da kuma kasa baki daya.
Ogbonnaya ya ce duk wanda yake shakkar abin da ya fada, ya duba sashin binciken yanar gizo na google, inda zai nemi rumbun binciken Majalisar dinkin Duniya mai taken: “Accelerating Africa to 2015, a report series to the UN special enboy for global education.”