✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta sanya Dani Ceballos a kasuwa

A ranar Talatar ce kulob din Real Madrid da ke Spain ya sanya dan kwallon tsakiyarsa Dani Ceballos a kasuwa. Kulob din ya sanya farashin…

A ranar Talatar ce kulob din Real Madrid da ke Spain ya sanya dan kwallon tsakiyarsa Dani Ceballos a kasuwa.

Kulob din ya sanya farashin Fam miliyan 45 (kimanin Naira biliyan 21 da miliyan 195) ga duk kulob din da ke bukatarsa.

Rahotanni sun nuna kulob din Arsenal da Tottenham dukkansu da ke Ingila suna rububi a kan dan kwallon.

Kulob din Madrid ya nuna zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Tottenham wajen yin musaya da Eriksen da Ceballos maimakon sayar da shi ga Arsenal.

Dani Ceballos dan asalin kasar Spain  ya zura kwallaye uku a raga a wasanni 23 da ya yi wa Madrid a kakar wasan da ta wuce. Sai dai Koci Zinedine Zidane ya nuna ba ya cikin ’yan kwallon da yake bukata a Madrid a kaka mai zuw, kuma hakan ya sa kulob din yake yunkurin cefanar da shi.

Ceballos zai cika shekara 23 a watan Agusta mai zuwa kuma ya taba yi wa kulob din Real Betis da ke Spain wasa kafin ya canja sheka zuwa Real Madrid.  Kuma yana wasa ne a tsakiyar fili.