✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Madrid ta samu sa’a ne kurum a kanmu amma mun fi karfinta – Angel Di Maria

dan kwallon gaba a kulob din PSG da ke Faransa, a shekaranjiya Laraba ya ce nasarar da Madrid ta samu a kan na PSG a…

dan kwallon gaba a kulob din PSG da ke Faransa, a shekaranjiya Laraba ya ce nasarar da Madrid ta samu a kan na PSG a ranar Talatar da ta wuce a gasar zakarun kulob-kulob na Turai, sa’a ce kawai ba wai Madrid ta fi karfinsu ba ne.

Wasan, wanda ya gudana a filin wasa na Bernebeu da ke Sifen, an tashi ne Real Madrid na da ci daya mai ban haushi.
Mun kai munanan hare-hare amma Allah bai nfa mun samu nasarar zura kwallo a ragar Madrid ba, amma dama daya da Madrid ta samu ne ta zura mana kwallo a raga”, inji Di-Maria.
Ya ce wasan da suka yi da Madrid shi ne wasa mafi kyau da suka buga tun da aka fara kakar wasa ta bana don haka ba za su damu ba saboda rashin nasarar da suka samu.
’Yan kwallon PSG Adrien Rabiot da Di Maria sun yi kokari a wasan, amma dan kwallon Madrid Nacho ne ya samu nasarar zura kwallo a ragar PSG jim kadan bayan ya canza dan kwallon baya na Madrid Marceelo bayan ya ji ciwo.
Yanzu kulob din Madrid ya haye zagaye na biyu a gasar bayan ya hada maki 10 daga wasanni hudu. Shi kuma kulob din PSG sai ya yi wasa na gaba ne zai san matsayinsa.