✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta raba motoci ga ’yan kwallonta saboda bikin Kirsimeti

Mahukuntan kulob din Real Madrid da ke Spain a ranar Litinin da ta wuce sun raba motoci kyauta kirar Audi ga  daukacin ’yan kwallon kulob…

Mahukuntan kulob din Real Madrid da ke Spain a ranar Litinin da ta wuce sun raba motoci kyauta kirar Audi ga  daukacin ’yan kwallon kulob din da kuma jami’ansu saboda murnar bikin Kirsimeti.

A duk shekara kulob din kan raba irin wadannan motoci ga ’yan wasansa da kuma daukacin jami’ansu a matsayin goron Kirsimeti.

Kamfanin hada motoci kirar Audi da ke Jamus ne yake samar da motocin a wata yarjejeniya da suka kulla da kulob din Madrid.

Kamar yadda rahoton da kafar watsa labarai ta Legit.com ta ruwaito, an nuna kowane dan kwallo a kungiyar ya zabi motar da ta fi kwanta masa a rai ne a yayin bikin ba su kyaututtukan.

Kyaftin Sergio Ramos ne ya zabi motar da ta fi kowace tsada inda aka kiyasta kudinta a kan Fam dubu 87 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 41 da dubu 325.  ’Yan kwallon Madrid irin su Eden Hazard da Dani Carbajal da Lucas Bazkuez da Toni Kroos da Nacho Fernandez da  James Rodriguez kuwa sun zabi mota ce da aka kiyasta kudinta a kan Fam dubu 74 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 35 da dubu 150.