✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta ki korar Benitez

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana cewa ya fasa korar kocinsa Rafael Benitez daga bakin aiki.  An yi ta rade-radin cewa za…

Kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana cewa ya fasa korar kocinsa Rafael Benitez daga bakin aiki.  An yi ta rade-radin cewa za a kori kocin bayan kulob din Barcelona ya lallasa na Madrid da ci 4-0 a gasar La-Liga a ranar Asabar da ta wuce.
Kulob din ya dauki wannan shawarar ce a taron manema labarai da ya kira a ranar Litinin da ta gabata, inda shugaban kulob din Florentina  Perez ya bayyana matakin da mahukunta kulob din suka dauka na cigaba da yin hulda da Benitez a matsayin koci.
Sai dai da yawa daga cikin magoya bayan kulob din ba su ji dadin wannan mataki da kulob din ya dauka ba inda tuni wasu suka fara tunanin daina goya wa kulob din baya.
Kocin ya fara shan suka ne daga wajen magoya bayan kulob din da kuma wasu daga cikin ’yan kwallon kulob din ciki har da Cristiano Ronaldo jim kadan bayan FC Barcelona ta lallasa Madrid da ci 4-0 a gasar La-Liga da ake wa lakabi da El-Clasico a ranar Asabar da ta wuce.
Haka kuma magoya bayan kulob din sun yi zanga-zanga a kori shugaban kulob din Perez a zaton su shi ke daure wa Benitez  gindi amma abin mamaki sai shugaban ya bayar da sanarwar cigaba da yin hulda da kocin, kuma ba za a sallame shi daga aiki a kulob din ba.
Hakan ta sa da yawa daga cikin magoya bayan kulob din suka nuna bacin ransu. Wasu ma sun sha alwashin daina mara wa kulob din baya muddin ba a sallami kocin ba.
Kawo yanzu Madrid ce take matsayi na uku a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar La-Liga ta Sifen.  FC Barcelona ce ta farko sai Atletico Madrid ke biye da ita sannan sai Real Madrid.
Yanzu dai duniya ta zuba ido ta ga yadda kulob din zai cigaba da fafatawa a sauran wasannin da suka rage masa a kakar wasa ta bana.