Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna mahukunta kulob din sun fara yunkurin cefano zaratan ’yan kwallo da zarar an bude kakar cinikin ’yan kwallo a watan Janairu.
Daga cikin ’yan kwallon da kulob din zai fi mayar da hankali wajen sayo su akwai Neymar da ke buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) da kuma dan kwallon Tottenham da ke Ingila Christian Eriksen.
Kulob din ya ce zai yi haka ne don ya karfafa gwiwar ’yan wasansa da yanzu haka suke fuskantar matsala tun bayan da Cristiano Ronaldo ya bar kulob din Madrid ya koma na Jubentus da ke Italiya a kakar wasa ta bana.
Neymar wanda ya canza sheka daga kulob din FC Barcelona na Sifen zuwa na PSG da ke Faransa kimanin shekaru biyu da suka gabata, rahotanni sun nuna akwai yiwuwar ya canza sheka zuwa kulob din Madrid idan ya samu damar yin haka.
Madrid dai ta shiga tsaka mai wuya tun bayan da ta buga wasanni 4 a jere ba tare da samun nasara ba.