Rahotanni daga kulob din Real Madrid da ke Spain sun ce kulob din ya fara yunkurin sayo dan kwallon Najeriya Samuel Chukwueze da yanzu ke buga kwallo a kulob din Billareal na Spain.
Kafar watsa labaran yadda ake cinikin ’yan kwallo a Spain ta Intanet mai suna Fichajes na daga cikin wadanda suka kalato wannan labari.
Kulob din Madrid dai na kokarin maye gurbin dan kwallon gabansa Gareth Bale ne da ake rade-radin zai bar kulob din a watan Janairu mai zuwa. Hakan ya sa kulob din yake tunanin Samuel Chukwueze ne ya fi dacewa ya maye gurbinsa.
Baya ga Madrid, rahotanni sun tabbatar kulob da dama suna zawarcin Chukwueze ciki har da kulob din FC Barcelona.
Samuel dan shekara 20 yana daga cikin ’yan kwallon da tauraruwarsu ke haskakawa a halin yanzu. Kuma yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles ta Najeriya.