Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Sifen Florentina Perez ya fara yunkurin maye gurbin shahararren dan kwallon kulob din Cristiano Ronaldo da Neymar wanda yanzu haka yake buga wa kulob din FC Barcelona na Sifen kwallo.
Rahoton ya nuna tuni shugaban ya nuna sha’awar biyan Neymar zunzurutun Yuro miliyan 35 kwatankwacin Naira biliyan 10 da miliyan 745 a shekara a matsayin albashi idan ya amince da tayin komawa Madrid din.
Kamar yadda wata jaridar labarin wasanni Diario Sport da ake wallafawa a Sifen ta kalato, an nuna shugaban yana kokarin sayar da Ronaldo ne don maye gurbinsa da Neymar.
Jaridar ta ce an ji shugaban na Madrid yana yin nadamar rashin sayen Neymar a shekaru uku da suka wuce kafin kulob din FC Barcelona ya saye shi.
Sai dai idan har Madrid ta ce za ta sayi Neymar a halin yanzu sai ta ajiye zunzurutun Yuro miliyan 190 kwatankwacin Naira biliyan 58 da miliyan 330 a matsayin farashin da kulob din FC Barcelona ya kakaba wa dan kwallon ga duk mai bukatar ya saye shi.
Ana hasashen shugaban Madrid din ya fara tunanin ajiye wadannan kudi don ganin ya dauke Neymar din ko ta halin ka-ka.
An ce shugaban yana yunkurin yin cinikin ne idan ya cefanar da Cristiano Ronaldo ga wadansu kulob da ke zawarcinsa irin su kulob din Manchester United da ke Ingila da kuma na PSG da ke Faransa.
Neymar, wanda yanzu haka yake tattaunawa da kulob din FC Barcelona a yunkurin tsawaita kwantaraginsa a kulob din, kocinsa Luis Enrikue a ranar Talatar da ta wuce ya ce yana da yakinin dan kwallon zai sabunta kwantaraginsa ba tare da wata matsala ba.
Kafin yarjejeniyar tsawaita kwantaraginsa a Barcelona ta kankama, shugaban Madrid Perez ya nuna sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi don ganin ya dauke Neymar daga kulob din, ganin cewa a watan gobe ne Ronaldo zai cika shekara 31 a duniya da hakan ya nuna ya fara tsufa a harkar kwallo.
Madrid ta fara yunkurin maye Ronaldo da Neymar
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke Sifen Florentina Perez ya fara yunkurin maye gurbin…