A safiyar yau Asabar ce Allah Ya karbi rayuwar Alhaji Musa Lawan Madakin Masarautar Tikau da ke Karamar Hukumar Nangere ta Jihar Yobe.
Marigayin mai kimanin shekaru 80 dai uba ne ga harkokin siyasar Jihar Yobe wadda jigo ne a jam’iyya mai mulkin Jihar jam’iyyar APC.
- Tawagar ECOWAS ta koma Nijar domin tattaunawa da sojin da suka hambarar da Bazoum
- ’Yan bindiga sun harbe mai fafutikar kare hakkin bakar fata a Brazil
Wakilinmu ya ruwaito cewa, marigayin ya kasance daya daga cikin ’yan siyasar da aka kafa jam’iyyar APC wanda tun lokacin jumhuriya ta biyu ake gwagwarmaya da shi cikin harkokin siyasar kasar nan.
Alhaji Musa Lawan shi ne jagorar jam’iyyar APC a shiyyar dan Majalisar Dattawa a mazabar Kudancin Jihar ta Yobe mai hedikwata a garin Potiskum.
An yi sallar jana’izar marigayin da misalin karfe 4.30 na Yammacin wannan rana ta Asabar a kofar gidansa da ke garin Potiskum.
Ya rasu ya bar iyalai masu tarin yawa cikin su har da Alhaji Bala Musa Lawan shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Potiskum.
Haka kuma, daga iyalan da ya bari akwai mai wakiltar Karamar Hukumar Nangere a zauren Majalisar Dokokin Jihar, Honabul Saminu Musa Lawan.