✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Macijiya mai ido uku ta bayyana a kan titi a Australia

Hukumomin kula da gandun daji sun yi ta rarraba wasu hotuna na wata macijiya mai ido uku da aka gani a kan wani babban titi…

Hukumomin kula da gandun daji sun yi ta rarraba wasu hotuna na wata macijiya mai ido uku da aka gani a kan wani babban titi a Arewacin Australiya.

Hukumar Gandun Daji ta Northern Territory ta bayyana lamarin, wanda aka yi ta yadawa a intanet, da wanda ba kasafai ake gani ba.

Macijiyar wadda aka sanya wa suna Monty Python, wadda kuma jaririyar mesa ce, ta mutu makonni kadan bayan da aka gano ta a watan Maris din da ya gabata.

Kwararru sun ce, idon macijiyar na ukun wanda ke tsakar kanta, ido ne na ainihi da ya samu daga sauyin halitta.

Masu yawon bude ido a daji ne suka gano ta kusa da garin Humpty Doo, kilomita 40 daga Kudu maso Gabashin Darwin.

Jami’ai sun shaida wa majiyar BBC cewa, a yayin da aka gano mesar mai tsawon inci 15, an gan ta tana ta gararambar neman abinci ne saboda tagwayen halittarta.

Hukumar Gandun Dajin ta ce, hoton jiki da aka dauka na macijiyar ya nuna cewa ba kai biyu ne da ita da suka hade ba.

A shafinta na Facebook hukumar ta ce, “Hoton ya nuna cewa akwai wata jijiyar mai lafiyayyen ido na uku.”

Wani kwararre kan harkar macizai Farfesa Bryan Fry sauyin halitta na daga cikin wani bangare na samuwar halittu.

“Kowane jariri yana samun sauyin halitta ta wani bangare – na wannan macijiyar dai ya samu tawaya ne,” in ji Farfesa Fry na Jami’ar Kueensland.

Farfesa Fry ya ce, “ban taba ganin maciji mai ido uku ba, amma muna da mesa mai kai biyu a dakin gwaje-gwajenmu – kawai dai wani irin sauyin halitta ne na daban daga wanda muka saba gani a tattare da ‘yan biyun da ake haifa a hade.”