✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maciji ya tilasta wa jirgin sama yin saukar gaggawa

An hangi macijin a cikin gurbin fitilar da take haska saman jirgin na Kamfanin AirAsia

An tilasta wa wani jirgin sama yin saukar gaggawa bayan wani ya ga maciji a cikin jirgin.

An hangi macijin a cikin gurbin fitilar da take haska saman jirgin na Kamfanin AirAsia.

Jirgin ya taso ne daga Kuala Lumpur Babban Birnin Malaysia zuwa Gundumar Tawau da ke Jihar Sabah a Malaysia.

Har yanzu dai ba a bayyana wanda ya fara ganin macijin ba, amma an sanar da matukan jirgin nan take, kuma Kyaftin din jirgin ya yanke shawarar yin saukar gaggawa a birnin Kuching don yin feshin magani a jirgin da kuma cire macijin.

Wani fasinja ya wallafa bidiyon macijin a manhajar TikTok mai suna E-dal Tay (@edal8808), yana cewa, kalli yadda macijin yake tafiya a inda fasinjoji ke
zaune a cikin jirgin sama.

Hoton bidiyon da aka wallafa mai ban tsoro ya samu kusan ra’ayoyin jama’a kusan miliyan uku da sharhi daga masu amfani da manhajar a duk fadin
duniya.

“Da gaske Maciji a cikin jirgin sama,” kamar yadda wani mai sharhi ya rubuta, yana kwatanta wani fim din da aka yi a
2006.

“Sabon shafin tsoro ya bude ga fasinjoji,” Wani kuwa cewa ya yi, “Wannan lamari ne mai ban tsoro kuma yana iya faruwa,” don hakan ya yarda da rahoton.

“Kamfanin Jiragen AirAsia na sane da
lamarin da ya faru a jirgin da ya tashi daga Kuala Lumpur zuwa Tawau,” Babban jami’in tsaro na Kamfanin
AirAsia, Liong Tien Ling, inda ya shaida wa tashar Labarai ta CNN ta Turkiyya lamarin.

Ya kara da cewa, “an sanar da Kyaftin din jirgin, nan take aka karkatar da jirgin zuwa birnin Kuching don yi masa feshin maganin da zai iya fitar da macijin.”

Ling ya kuma ce matuqin jirgin ya dauki matakin da ya dace, ta hanyar ba da fifiko ga lafiyar fasinjoji da ma’aikatan jirgin ya kuma ambata cewa, bai san yadda maciji ya shiga cikin jirgin ba, inda ya bayyana faruwar hakan da abun mamaki.

“Wannan lamari ne da ba kasafai ya fiya faruwa a jirgin sama”.

Ling ya kara shaida wa Kafar Labarai ta Channel NewsAsia cewa, “Kyaftin din ya dauki matakin da ya dace. Bai bata lokaci ko neman amincewar fasinjoji ko ma’aikatan jirgin da suke ciki wajen sanya rayuwarsu a hatsari ba.”