✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mace na iya maye gurbin Buhari a 2023’

Na yi imanin cewa mata za su karbi wurinsu a matsayinsu na shugabanni.

Shugaba kuma wacce ta assasa kungiyar kare muradun mata ta Aspire Women Forum, Barista Zainab Marwa-Abubakar, ta ce akwai yiwuwar mace na iya cin gajiyar kujerar Shugaba Muhammadu Buhari.

A daya daga shirye-shiryen bikin tunawa da ranar Mata ta Duniya ta International Women’s Day, Barista Marwa ta fadi haka ne a ranar Lahadi yayin wani taron masu ruwa da tsaki na mata da aka gudanar a Abuja.

A cewarta, “yayin da shekarar 2023 ke karatowa, na yi imanin cewa mata za su karbi wurinsu a matsayinsu na shugabanni, masu tsara manufofi da yanke shawarar a madafan iko.”

“A yanzu haka bamu gama hada kanmu ba wajen zabar mace ta gaji mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.”

“Sai dai hakan ba wata matsala bace domin komai yana iya faruwa, kuma nan da zuwa wani lokaci hakan na iya kasancewa,” in ji Barrista Zainab yayin furucinta kan samun mace wacce za ta zamo Shugabar Kasa a zaben 2023.

“Ya zama wajibi mu mata mu tashi mu nemi ilimi musamman a yanzu da siyasa ta zama gama gari, saboda haka ya kamata kowace mace ta nemi wata jam’iyyar siyasa ta yi rajita da ita.”

“Ni jam’iyyata ita ce APC kuma a yanzu haka tana gudanar da rajistar ga dukkanin mambobinta a fadin kasar. Saboda haka ya kamata mu je mu yi rajista da kowace jam’iyya muke sha’awa don tun a yanzu mu fara shirya tsare-tsare da manufofi.”

Barista Zainab wacce diya ce ga tsohon Gwamnan Jihohin Legas Borno a lokacin mulkin soji kuma wanda ke zaman Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Birgediya-Janar Muhammad Buba Marwa, ta kuma ce ana iya amfani da siyasa wajen wayar da kan al’umma kan illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi.