A karshen wancan mako gamayyar kungiyoyin kasa da kasa irin su Asusun kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF da Bankin duniya da shashen Majalisar dinkin duniya da ya ke kula da yawan al’umma wato UNEPA da suke bin diddikin mace-macen kananan yara da shekarunsu su ka kasance zuwa biyar da haihuwa, sun yi hasashen cewa idan har abubuwa suka ci gaba da kasancewa a yadda suke yanzu a wasu kasashen duniya, musamman masu tasowa, to, kuwa ba makawa irin wadancan kananan yara miliyan 60, za su mutu tsakanin wannan shekarar ta 2017 zuwa 2030, wato ke nan nan da shekaru 12 masu zuwa, har suka kara da cewa akasarinsu za su kasance sabuwar haihuwa ne.
Rahotan wadancan kungiyoyi da suka fitar a Abuja ya tabbatar da cewa kasar Indiya, ita ke kan gaba a mace-macen kananan yara da kashi 24, cikin 100, yayin da kasar Pakistan na da kashi 10, cikin 100, yayin da kasar nan (Nijeriya), take ta uku a kashi 9 cikin 100. Ma fi yawan mace-macen kananan yara inji rahotan yana faruwa ne a kasashen kudancin Asiya da suke da kashi 39, cikin 100, yayin da kasashen Kudu da sahara na Afirka suke da kashi 38 cikin 100 na mace-macen. kididdigar ta tabbatar da cewa yara 15,000, suka mutu a bara (2016) a duniya baki daya, kafin sukai shekaru 5, kuma kashi 46 cikin 100, na mace-macen kananan yara sun faru ne cikin kwanaki 28, na haihuwarsu.
Idan muka koma ta mace-macen mata masu juna biyu, a shekarar 1990, da Majalisar dinkin duniya da kungiyar lafiya ta duniya WHO da sauran kungiyoyi da kasashen duniya su ka bullo da shirin shekaru 15, wato zuwa 2015, mai sunan CIMMA MUARADN kARNI wato MDG, shirin da ya kuduri aniyar yaki da matsaloli irin su samar da wadatacce kuma tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli da inganta samar da ilmi tun daga tushe da kuma rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara. A waccan shekara ta 1990, mata 543,000 suka mutu a duniya baki daya, amma sai ga shi a shekarar 2013, shekaru hudu da fara shirin na MDG, adadin ya dawo zuwa mata 289,000, su ka mutu a dukkan fadin duniya, amma kuma zuwa shekarar 2015, da kammala shirin, adadin mace-macen mata masu juna biyu ya sake hawa zuwa 500,000, a wannan shekarar. An kuma kiyasta cewa a duk cikin minti biyu, mace daya ke mutuwa a duniya a dalilin mace-macen mata masu juna biyu. A wannan fanni ma kasar Indiya da kasar nan suke da 1 cikin 3, na mata masu juna biyu da suke mutuwa a duniya.
Alhali a lokacin da aka fara shirin na MDG, aniyarsa, ita ce ya rage mace-macen mata masu juna biyu da a kalla kashi 75 cikin 100, a tsakankanin kasashen duniya da suke fama da wannan mummunar annoba. Amma sai ga shi kasashe 19, irin su Labanan da Nepal da Ruwanda suka kasance kasashen da suka kai bantansu na samun waccan nasara. kasashe 63, kuwa suna kan hanyar cimma nasara, yayin da wasu 13, ba su samu wata nasarar da za a je a karas ba. kasar nan kuma zuwa wannan lokaci, ita ke da kashi 10 cikin 100 na yawan mace-macen mata masu juna biyu a duniya baki daya. Alal misali a shekarar 2015, daga cikin dukkan mata 100,000, da su ka haihu a kasar nan 814, suka mutu, alhali a kasashen da ke makwabtaka da mu irin su Ghana, a duk cikin mace 100,000, da ta haihu 350 su ke mutuwa, yayin da a jamhuriyar Nijar mata 590, a duk cikin 100,000, da suka haihu suka mutu a waccan shekarar.
Ko kusa ba na son in kawo kididdigar matan da suka mutu a sanadiyyar haihuwa a kasashen da su ka ci gaba kasancewar bindin rakumi ya yi nisa da kasa sai in ya kwanta, wannan rakumin kuma ba zai kwanta ba. Alal misali a kasa Italiya mata 4, rak suke mutuwa daga cikin mata 100,000, da suka haihu suka mutu. Haka labarin yake a kasar Girka, inda mata 3, kacal suka mutu daga cikin mata 100,000 su ka haihu a kasar a shekarar 2015. A kasar Saudiya ma mata 24 suka mutu a wajen haihuwa a cikin 100,000 da suka haihu. Mu kuwa a nan kasar idan ka bi ta shiyya-shiyya, shiyyar Arewa maso gabas ita ke kan gaba a mace-macen mata masu juna biyu a cikin sauran shiyyoyi biyar na kasar nan da mata 1,549, daga cikin mata 100,000, da suka haihu sai shiyyar Arewa maso Yamma na bi ma ta. A shiyyar Kudu maso Gabas kuwa mata 286, daga cikin 100,000, su ka haihu suka mutu. Daga shiyyar Kudu maso Gabas kuwa mata 165, daga cikin 100,000, da su ka haihu a bara waccan suka mutu kamar yadda kididdigar masana kiwon lafiya na kasar nan suka fitar.
Mai karatu, idan ka yi duban tsabta daga wadannan alkaluma da ake amfani da su a duniyar masana kiwon lafiya za ka fahimci cewa mahukuntan kasar nan da mutanenta, musamman na shiyyoyin Arewa uku, wato shiyyar Arewa maso Gabas da shiyyar arewa maso yamma da shiyyar Arewa ta tsakiya suna da gagarumin aiki wajen tunkarar yaki gadan-gadan a kan matsalolin da suke haddasa wannan mummunar annoba ta mace-macen mata masu juna biyu a yayin haihuwa da kuma mace-macen kananan yara.
Matsalolin kamar yadda masana kiwon lafiya su ka bayyana, sun rataya ne akan mahukunta kama daga Majalisun kananan Hukumomi zuwa Gwamnatocin jihohi da Gwamnatin tarayya kasancewar samar da kiwon lafiya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya bayyana, ya rataya a kan wadannan Gwamnatoci uku.
Mu ma mutanen kasa masu iyali muna da namu laifin. A lokacin da Gwamnatocin kasar nan ba su iya samar da ingantattun asibitoci manya da kanana ta wadata su da kwararrun ma’aikata da kayayyakin aiki da magunguna da sauran bukatu na yau da kullum ga ma’aikatan kiwon lafiya kamar jin dadin rayuwarsu da horarwa akai-akai da kulawa da yadda ma’aikatan ke gudanar da ayyukansu, to ko ba yadda za a yi ayyukan kiwon lafiya su inganta a kasar nan.
Mu kuma mutanen kasa musamman na jihohin shiyyoyin Arewa uku, muddin ba mu canja dabi’ar mu ba ta hana matan mu su je asibitoci komai lalacewarsu don awon ciki da sauran bukatu na kiwon lafiya a lokacin da ya kamata, to kuwa za mu ci gaba da zama kurar baya a cikin matsalolin mace-macen mata masu juna biyu da cututtukan da kan kashe kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa.
Da wannan ke nan ashe ka ga ya kamata mai karatu mutanen kasa su rinka dagewa wajen matsa wa zababbu da nadaddu da sauran wakilansu wajen tabbatar da cewa suna masu ayyukan da za su inganta rayuwarsu ta fannin kiwon lafiya da makamantansu, babu dalilin da zai sa su yi ta binsu don neman biyan bukatun kashin kansu. Ta haka kawai za mu more mulkin dimokuradiyya.