✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mace-macen Kano: Sakamakon bincike sun yi karo da juna

Sakamakon binciken da Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar kan mutuwar sama da mutum 1,700 da aka samu a jihar ya ci karo da na Gwamnatin…

Sakamakon binciken da Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar kan mutuwar sama da mutum 1,700 da aka samu a jihar ya ci karo da na Gwamnatin Tarayya.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi watsi da sakamakon binciken mace-macen da kwamitin Gwamnatin Tarayya ya gudanar wanda ya nuna cutar coronavirus ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 na mutanen wanda ya kai ga mutum 587.

“Matukar ba za a iya dogaro da sakamakon bincike ba, to sai a yi watsi da shi”, inji shi yayin da yake magana game da sakamakon binciken Gwamnatin Tarayya.

Sakamako ya bambanta

Rahoton kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya ce kashi 15.9 na mamatan ne suka rasu sakamakon rashin lafiya da ke alaka da cutar coronavirus.

Rahoton na Kano na zuwa ne kimanin makonni biyu da bayan Ministan Lafiya Osagie Ehaniya ya gabatar da na kwamitin Gwamnatin Tarayya.

Shugaban tawagar masu binciken na Jihar Kano, Farfesa Mukhtar Gadanya na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, ya ce mutum 255 ne a cikin mamata 1,774 suka rasu sakamakon rashin lafiya mai alaka da coornavirus.

Alkaluman sun saba da na Kwamitin Gwamnatin Tarayya wanda Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya gabatar da ya nuna cewa cutar coronavirus ta kashe mutum 587.

Ganduje ya ja da sakamakon binciken Gwamnatin Tarayya

Da yake karbar rahoton binciken da kwamitin ya gudanar ta hanyar tambayar shaidu baka-da-baka, Gwamna Abdullahi Ganduje ya yaba wa kwamitin bisa namijin aikin da suka yi, wanda ya ce yana kunshe da alkaluma masu gamsarwa da saukin fahimta.

Gwamnan ya kara da cewa shi da kansa zai mika sakamakon ga Shugaba Muhammadu Buhari da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma MInistan Lafiya.

Alkauman binciken Kano

Farfesa Gadanya ya ce kashi 70 na mamatan sun rasu ne ta dalilin hawan jini, cutar suga da wasu cututtuka masu kisa. Kashi 76 dinsu kuma ‘yan shekaru 50 zuwa sama ne.

Ya ci gaba da cewa mutum 1,774 ne suka rasu daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan Mayu, 2020 a kananan hukumomi takwas da ke kwayar birnin Kano.

1,004 daga ciki sun rasu ne sakamakon zazzabi, sarkewar nunfashi kuma ta kashe mutum 59, wasu 69 kuma suka rasu sakamakon tsanantar rashin lafiyar da suke fama da ita, sai kuma 567 da ba su yi ko da zazzabi ba.

Kahsi 60 na mamatan maza ne, sauran kashi 40 din kuma mata, a cewar rahoton.