✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudi na 4: Kula da rainon maigida cikin Salo

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili,  da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili,  da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayanin darasi na 4 a makarantar Mowar Mata, wacce Malama Bushirah ke gabatarwa. Bayan ta yi sallama dalibanta sun amsa, sai Malama ta fara bayani:
A yau insha Allah za mu yi bayani akan makulli na 4 wajen budewa da bankado soyayyar maigida zuwa gareki. Wannan makulli kuwa shi ne gabatar da so da kulawa ga maigidanki cikin kauna, ta hanyar jiji da shi, tattalinsa, jin tausayinsa da samar masa da dukkan kulawar da yake bukata gauraye da kauna a kodayaushe. Ga yadda uwargida za ta aiwatar da wannan:
1. Maida shi dan lele: Masana hikima da masana kimiyyar dabi’un dan Adam na kamanta bukatar maigida a wajen uwargidansa kamar bukatar dan karamin yaro ne a wajen uwarsa, yaron ma wanda yake shi ne dan lele, mafi soyuwa a cikin zuciyar uwarsa daga cikin sauran ‘ya’yan, kuma sannan mafi karanta daga cikinsu duka. Tilas ne za a tarar da wannan uwa tana jijji da dan nan sosai, tana tattalinsa tana kokarin faranta masa rai a kodayaushe, kullum burinta ta jiyar da shi dadi taga murmushinsa, in ransa ya baci za ta lallasheshi da kalamai masu dadi ga kunnuwansa kuma wadanda za su kwantar masa da hankali. In ya nemi wani abu za ta kai gwauro ta kai mari don ganin ta samar masa da abin nan. Tana masa kallo da fara’a cikin kauna kuma tana alfahari da shi a kodayausheshi, ko ya yi mata wani laifi ba ta jin haushinsa a zuciyarta, kila sai dai ta ji haushin laifin kadai. To kamar haka ya kamata ku rika yi wa mazanku in kuna son ku bude dukkan soyayya da kulawarsu gareku. In kuka dage da aikata haka, komai tsanani komai dadi, to za ku ga yadda mazanku za su makale maku kamar misalin yadda karamin yaron da uwarsa ke jiji da shi zai makale mata, ba ya son nesa da ita, komai ya samo wajenta zai nufo kuma ko wa ya bata masa rai wajenta dai zai nufo don neman sauki, itace wajen samun aminci da natsuwar zuciyarsa, to haka mazajenku za su rika yi maku. Da yawa za ku ji ana cewa wasu matan sun asirce mazajensu, alhali ba asiri ba ne, wannan sirrin ne suka gano suke aikatar da shi cikin rayuwar aurensu.
2. Maida shi Sarkinki, ke kuma baranyarsa: A nan ba ana nufin ki rika sunkuya masa kina kirarin sunkuye masgaye da gyara kimtsi da kyau ba, (duk da cewa kina iya wannan a wani bangare in ta kama). Ana nufin kamar yadda Sarki na sama kuma gaba da kowa a wajen barorinsa, maganarsa dole su saurareta cikin natsuwa, umarninsa dole su yi aiki da shi, dokokinsa ba su isa su ketaresu ba, bukatarsa na sama da bukatun kansu, to ke ma haka ya kamata ki rika yi ga maigidanki in har kina so ki bude dukkan kofofin soyayyarsa da kulawarsa zuwa gareki. Domin shi sarkinki ne, shugabanki ne, gwamnankine kuma ja gabankine. Don haka mai da mijinki Sarki, shi kuma zai maida ke Sarauniyarsa.
3. Maida shi Oga, ke kuma sakatariyarsa: Ku lura da irin tsananin ladabin da sakatariya ke wa oganta, da irin taka tsantsan din da take yi wajen hulda da shi don ganin cewa ba ta saba masa ba, to ke ma haka ya kamata ki rika mu’amulantar maigidanki.
4. Da yawan matan aure nasa wasu al’mura na rayuwa sama kuma gaba da kula da mazajensu na aure, wasu matan kula da gida yana gaba da kula da mazansu, wasu kuma kula da ‘ya’yansu ya fi kula da mazajensu a wajensu, yayin da wasu kuma aikinsu ko harkar neman kudinsu sh ine gabansu ba kula da mazan aurensu ba. Wannan babban kuskure ne, muddin mace tana son ta mallake mijinta, dole sai ta mallaka masa lokaci, hankali da tunaninta gabadaya, sai ta sanya shi ya zama na farko gaba da kowa a rayuwar ta. Sai ta ba shi kulawa sama da kulawar da take ba kowa da komai a rayuwarta. Addini da bautar Allah shi ne abu na farko a rayuwar kowane Musulmi, don haka bayan mace ta kula da tsayar da addininta, abu mafi muhimmaci da ya kamata ta rika baiwa cikakkiyar kulawa da muhimmaci shi ne kula da biyan bukatun mijinta duka na zahiri da badini, ku sani kula da miji ibada ce mai matukar muhimmanci wacce ke iya kai mutum Aljannah ko kuma cikin azaba da fushin Allah.
Sai sati na gaba, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.