Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, Insha Allahu za mu cigaba da bayani akan darasin farko na makarantar mowar mata daga inda muka tsaya a makon jiya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu, amin.
Wata daga can baya ta daga hannu alamar tana son yin tambaya. “Bismillah Zainab…” “Malama to in abinda mijin mutum yake yi babban zunubi ne fa? Kamar caca, shan giya ko neman mata, shi ma wannan ajizancin da dole ne mace ta amince da shi wajen mu’amularta da mijinta?”
“Yana da matukar muhimmanci ga macen da ke son bude so da kaunar mijinta gaba dayanta ta aminta da dukkannin ajizancinsa kamar yadda ta aminta da sauran kyawawan halayensa. Amma mu sani cewa zama da miji ko mata mai aika manyan zunubbai, yana da hukuncinsa na musamman a kyakykyawar shari’armu ta Musulunci. Akwai matakan da matar ko mijin zai bi don magance wannan matsala. Amma nan ba hurumin wannan bayani ba ne kar mu fita daga maudu’in dake gabanmu.”
“Malama don Allah a taimaka a yi mana bayani game da haka domin da yawanmu muna fama da mazaje masu aika manyan zunubai musamman neman mata, da sauransu.” daliba Hajiya Umma ta tambaya bayan ta daga hannu an ba ta izinin yin tambaya.
“Mataki na farko shi ne ki fahimci cewa wannan aikin sabo da yake yi ba ke ya sabamawa ba, Allah Ya sabamawa, don haka ba ki da hurumin da za ki rika jin haushinsa kina kullatarsa kina masa bita- da- kulli, kina hukunta sa ta hanyar munanan halayya gareshi, ba ki da wannan hurumin na kashin kanki, sai dai ki ji haushin ketare iyakokin Allah da yake yi kamar yadda za ki ji haushi in wani ne ya yi haka ba mijinkiba. Sai dai ki yi bakin cikin cewa mijinki ya kama hanyar halaka ba ki rika jin haushin cewa mijin manemin mata ne, ko dan cacane, da sauransu.
Mataki na biyu sai ki binciki kanki, da wuya miji ya zama mai aikata wani babban alkaba’iri ya kasance matarsa Salihar mace ce. Yawanci in miji manemin matane za ka tarar matarsa mushirika ce, watau ba ta da cikakken tauhidi, in mijine yake shirka sai ka tarar matarsa mazinaciya ce kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada cikin Aya ta 3 da ta 26, Surah ta 24: “Mazinaci ba ya aure face da mazinaciya ko mushrika, mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci ko mushriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai. “
“Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma miyagun maza domin miyagun mata suke, kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza, tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. Wadannan su ne wadanda ake barrantawa daga abin da (masu kazafi) suke fada, kuma suna da gafara da arziki na karimci.”
Don haka mataki na biyu shi ne uwargida ta gyara kanta ta zama Salihar mace, indai akwai sauran rabon zama a hankali mijinta Allah zai shiryar da shi ya zama salihi cikin yardar sa.
Mataki na uku shine yawan yi masa addu’a da nema masa gafarar Ubangiji da kuma yi masa sassaukar nasiha cikin fahimta da so da kauna ba cikin jin haushi da nuna kyama ba.
Mataki na hudu in aikin zunubin ya yi kamari, kuma uwargida ta dade tana kwatanta matakai ukun da suka gabata a sama amma mijin bai canza ba, to sai ta gabatar da maganar ga magabata amma a sirrance, ya kasance su kadai suka san abin da ke faruwa don a kira shi a yi masa fada.
Mataki na biyar shi ne rabuwa da shi ta hanya ma fi dacewa in har an yi amfani da duka wadannan matakan amma ya ki daina aikata wannan alkaba’irin domin haramun ne zaman aure da mutum mai aikata manyan zunubbai.
Sai sati na gaba Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.