✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudan Soyayyar Maigida 3

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga cigaban bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda kullum…

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga cigaban bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda kullum zai kasance tsundum cikin kogin so da kaunarta kuma zai rika marmarinta, ya kasance ba ya son rabuwa da ita kuma duk abinda take so zai yi mata.

Mowar Mata, Cigaba…
Amma kafin in ce tak Bushira ta mike a zabure: “Waye ya ji kunyar? Jin kunya ta wuce ta gidanku? Kakanki ba kwarton matan aure ba ne? An sha kama shi a gidan matan mutane? Ke kuma jin kunya ta wuce na wan Ubanki da aka kama shi ya yi ma sa‘ar jikarsa fyade?  Sannan ke Yayarki da kuke Uba daya ba sai da ta yi cikin shege ba ta haife shi? Ke kuma kanen Uwarki ba barawon tumaki ba ne? Har kuna da bakin da za ku ce ma wani bai da kunya…“
Ta bi su ta yi musu tatas.   Zagi irin wanda ban taba ji ba, kuma wanda ban taba zaton zai fito daga bakin Bushira ba ranar sai da ta yi musu shi, sannan ta rufe da: “Karuwanci da mijinku, mijina yanzu na fara, da somin tabi na yi, amma yanzu za ku san ina karuwanci, kuma duk shegiyar da ta kara shigo min daki ranar aiki za ta ci…Ku fita ku ba ni waje… “
Ta ingiza su wajen daki ta maida kofa ta rufe, suna  fita suka fashe da kuka na borin kunya wanda nan da nan na ji makwabta sun fara kwankwasa kofa. Nayi sauri na je nace da su ba komi sannan suka juya suka tafi.
Na dawo daki na iske Bushira ta juya mini baya…  Ai yau…, ban karasa ba ta ballara min wata irin bakar harara wadda har sai da gabana ya fadi…
“Me za ka ce? Duk wa ya janyo wannan in ba kai ba? A gabanka suke wulakanta ni suna zagina ta uwa ta uba amma ba ka taba ce masu komai ba a matsayinka na shugaba, amma da a ce nic e da zuwana na fara yi masu irin yadda suke min da tuni ka taka min birki, ka ce zan wulakanta maka mata ko? To daga yau sai yau! Na gama daukar duk wani cin kashi daga wajen matanka, don haka in za ka saita su ka yi, in ba haka ba shege ka fasa ni da su…!!!“
Ni ma haka na kasa cewa komai, sumui sumui na wuce na yi alwalla na ta fi masallaci.
Tun daga ranar Bushira ta fita harkar mu ni da matana, ko amsar girki ta daina yi, da kyar na samu Mama Amurka ta lallasan min ita ta fara sakin jiki da ni. Bayan wata uku da faruwar haka ta haifi da namiji sambalele, wanda ko ni ban san da cikin ba sai da ya tsufa.
Su kuwa su Haulatu sai ga shi sun zo suna ta neman shiri da ita, suna shishshige mata har Barira na ba ta yayen yaro, Haulatu kuwa na haihuwa ta ce a sanya wa yarinyar suna Bushira. Da haka dai suka zo suka shirya suka hade kansu, da ma zafin kishi ne ya canza mini matana, amma suna da kyawun hali kuma ina sonsu sosai, yanzu ga shi kishiya ta yi mani saitinsu sun dawo daidai.
Bayan sun hada kansu su duka sun dawo abokanan juna, sai na shawarci Bushira akan ta rika koyar da su karatu da sauran abubuwan wayewa wadanda ta lura za su amfana da su. Ta ce da ma tana tunanin hakan. Ta fara koyar da su karatun Alkur’ani da tajwidinsa da kuma darussan Larabci.   A hankali kuma cikin wayau da basira irin nata, sai ta fara gyara masu abubuwan da ta lura suna kuskure cikin yanayin da suke mu’amularsu da ni. A hankali shi ma wannan sai ya zama wani darasi na musamman, wanda a hankali kuma ya zamar masu wata hanyar wasa da nishadantar da juna: Kowaccensu tana koyar da sauran abubuwan da ta fi kwarewa wajen shagaltar da da namiji da budo soyayya da kulawarsa.
Ba wanda ya kai ni mijinsu cin moriyar wannan abin alheri da Allah ma?aukakin Sarki Ya albarkaci matana da shi. Na zama mai kishirwar kasancewa da mata kodayaushe.   Duk inda nake nakan kosa na dawo gida wajen iyalina. Kulawa, soyayya da kyakkyawar mu’amular da suke nuna min ta kara min karfin mazantaka da jiji da kai irin na da namiji. Ya kara min kaifin hankali da basira a cikin dukkan al’amurana na rayuwar duniya. Wannan ya bude min kofofin arziki ya kuma hore min damar yin abubuwan cigaba kala daban- daban.
Wata sa’ar matana sukan hadu su kayatar da ni gabadayansu.   Su kan shirya mini tarba ta ban mamaki akai-akai, musamman in na yi tafiyar kwanaki, to duk ranar da na dawo tabbas zan tarar da sun shirya min wani abin kayatarwa mai ban mamaki.
Ana haka sai kanwar Haulatu ta samu matsala cikin rayuwar auren ta da mijin ta har ya yi mata saki daya. Bayan sun ji irin matsalolin da suke haifar masu da matsala ita da mijin ta, sai Bushira ta bayar da shawarar su koyar da ita abubuwan da suka koya wa junansu don ta gyara aurenta da mijin ta. Don haka suka hada kai suka rika koyar da ita abubuwan kayatar da rayuwar aure.   Sai ga shi da ta fara aikatawa, kafin iddarta ta cika mijin ya mayar da ita kuma aurensu ya dawo kamar na sabbin ma’aurata.
Daga nan, duk matar da suka ji tana da matsala a gidan aurenta, daga ‘yan uwa da makwabta, sai su koyar da ita wadannan darusssa, da haka har wannan makaranta ta bunkasa ta watsu a garuruwa, ta yi suna musamman ta fannin duk matar da ta aikatar da su cikin aurenta yana kawo mata kayataccen canji a cikin zamantakewar aurenta.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.