✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudan Soyayyar Maigida 2

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda…

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda kullum zai kasance cikin kogin so da kaunarta kuma zai rika marmarinta, ya kasance ba ya son rabuwa da ita kuma duk abinda take so zai yi mata.

Mowar Mata, Cigaba…
Bayan aurenmu ne Bushira ta ba ni babban al’ajabi, ta rikide ta koma irin macen da ban taba zaton za ta iya zama ba; ta koma irin macen da kowane namiji zai yi mafarkin a ce ya samu. Yadda Bushirah take da kunya da kankan da kai, sai ga shi ta koma Bushirah mai yin duk wasu abubuwa da mata ke yi don rikirkita kwakwalwar namiji.
In ta fara yi min shagwaba zuciya ta kan narke ta cika da dadi mara misaltuwa. Kowace irin magana za ta yi min cikin yatsina da tausasa murya take min. In ta nufo ni za ta kawo min abinci ko wani abu haka za ta taho tana taku daidai tana yatsina tana salon jan hankali kala-kala. Kallon kuwa da take min ina jin tana gauraya shi da wani sinadari dake sa ni inji na cika kuma na kai na kawo a matsayina na da namiji. Magana kuwa irin muryar da salon da take min magana ce daban da ta kowa. Kusan iri daya da yadda take wa yara kanana magana sai dai ni akwai wani karin taushi na musamman a cikin salon da take min magana da shi, don haka ko cikin fushi take min magana wannan taushin na nan a kodayaushe.
Sannan wani abu dake burge ni da Bushirah shi ne tsarkin yarintar ta na nan cikin halayya da dabi’unta don haka komi irin na yara take yi. Ko wani abu za ta tambaye ni irin yanayin da ‘yar karamar ‘ya ta Zarah za ta tambayeni ita ma haka take. Kuma in ta yi fushi irin na yara take kuma ba ta riko kamar yadda muka san kananan yara ba su da rikon laifi. Kullum hirar ta mai kayatarwa ce gareni ba ta damuna da labarai marasa kayatarwa ba kuma tana lura da yanayina, tana tantance bukatuna ta gabatar min da su daidai da yanayina. Irin yadda take min yakan sa in yi tunani lallai da Allah Ya kaddaro min itace macen farko da na fara aure, to zai yi wuya in kara wani auren.
Waje daya ne kawai Bushirah ta yi rauni gare shi shi ne wajen yin kwalliya da iya sa kaya.   Kwata-kwata ba ta son kwalliya ko kadan. Sauran matana kuwa gwanayen kwalliya da iya sa kaya ne da yin shiga ta dinkuna kala kala. Kullum in zan fita za su fito kowaccensu ta ci gayu da kwalliya tana kamshi, ita kuwa Bushira sai ta fito da daya daga cikin manyan dogayen rigunan da kullum a cikinsu take. Tunda ta zo gidana haka kowa ya saba ganinta ko kishiyoyinta ba su taba ganinta cikin wasu kaya ba sai wannan dogayen rigunan. Wanda hakan ya zame mata abin gori a wajensu. Amma na san da sun san irin kayan da take sawa a kasan dogayen rigunanta, to da sai sun ciji baki. Saboda zama Amurka da suka yi, Bushirah ta fi sabawa da irin kayansu. Don haka kodayaushe sune a jikinta, sai in za ta fito tsakar gida ko in ta yi baki sai ta dora doguwar riga ta rufesu. Na yi mita har na gaji ta rika sa kayan Hausawa amma ta kasa.
Wani kyakykyawan hali na Bushira kuma shi ne ita mai son kyautatawa da jiyar da dadi ce ga kowa ba ga mijinta kadai ba, don haka har kishiyoyinta, tana  kyautata masu da ba su hakkinsu, kuma tana taka- tsantsan kwarai wajen ganin ba ta shiga hakkinsu ba ko yaya ne.   Misali, in ba ranar aikinta ba ne, to in ba ni ne na neme ta ba, ko ganinta ban yi; kuma in suka je unguwa, in dai ba su bar mata sallahun in na dawo ta yi mini wata hidima ba, to ba za ta yarda ta kula ni ba. Wannan halin na taimaka min wajen tsayuwa da yin adalci a tsakanin matana.
Amma duk da haka ba ta tsira ba a wajen su Barira da Haulatu, tun suna yi mata habaici, har ta kai suna yi kiri-kiri, a gabanta, a gabana, a gaban yara, a gaban baki, za su yarfa mata magana mai daci, amma ba ta ramawa.Maganganu irinsu:
-’yar kilaki, jikar kilaki
-Ai digirin ma na kilakanci ne shi ya sa ba ta da abinyi sai karuwanci da mijin mutane…
-An gama feleke a duniya an zo an aure mana miji ana nuna an fi mu iko da shi.
-Wai sunan an sauke kur’ani ke nan, amma ba abinda ake sai iskanci da mijin mutane…
Sannan da ta yi shekara 2 ba ta samu haihuwa ba, sai suka koma yi mata gorin haihuwa:
“Yo ai mu da ma wata ‘yar burgumar akuya Maigida ya sayo mana da wannan matar, ko banza in akuya ce da yanzu an karu da ita. Da sauran ire-iren haka.”
Wata rana da yamma ina tare da Bushira muna hirar nishadi muna dariya, kawai sai ga su sun fado cikin dakin ko sallama babu:
“To, ana nan ana karuwanci da mijin mutane ko! Abinda aka iya ke nan!“  “Ke dai bari Yaya! Mts, an dai ji kunya!!!”
B ani son hayaniya da ka-ce na-ce, shi yas a ban taba tanka masu ba in suna irin wadannan maganganun, addu‘a dai nake yi musu Allah Ya ganar da su, amma yau na yi niyyar in taka masu burki.  Amma kafin in ce tak Bushira ta mike a zabure…
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.