✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudan Soyayyar Maigida (11)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani cikin darasi na 2 a makarantar mowar mata daga…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani cikin darasi na 2 a makarantar mowar mata daga inda muka tsaya a makon jiya.  Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a ciki, amin.
Malama Bushirah ta cigaba da bayani kamar haka: “Ga wannan jerin kyakkyawan halaye da dabi’u nan na maza don ya taimaka maku wajen yin ‘list’ din kyawawan halaye da dabi’un mazajenku. Sai a bi su daya bayan daya, duk wani hali da dabi’a da kika fahimci maigidanki ya mallaka daga cikibsu, sai ki rubuta shi a cikin littafin yabon mijinki. Ki nemo wasu ma wadanda ba a zana a nan ba in dai kin tabbata maigidanki yana mallakinsu sai ki rubuta su a ciki.
Misalan kyawawan halaye abin yabawa sun hada da: Mai kokari a cikin dukkan al’amuransa; mai hanzari wajen zartar da abubuwa; mai saurin fahimtar al’amura; mai tsara magana daki- daki; mai fasaha; kyaun kira; mai maida hankali; mai cikar iko; mara tsoro; mai cike da banantaka; jarumi; mai saurin fahimta; mai dubarar sarrafa kasuwanci da neman kudi; natsatstse; kwararre; mai nuna kauna da kulawa; mai burgewa da sa dadin zuciya; mai sakin fuska; mai son yara; mai tsafta; mai kwantar da hankali da sa natsuwa; mai cike da kasaita; mai kiyaye doka da oda, mai bin kai’ida; mai hankalta da abubuwa ; mai kwanciyar hankali; mai bada goyon baya; mai yawan kyauta, mai kyautatawa; masani; mai alkunya; abin dogaro; mai dagewa; mai rikon amana; tsayayyen namiji; abin darajtawa; azzakakuri; mai kamun kai; mai bin komi a hankali; na musamman; mai iya shiga ko iya sa kaya;Hakimtacce; mai himma; mai ilmi; mai cika aiki; wayayye; mai iya magana; mai karfafa gwiwa; mai nishadantarwa; adali; mai rikon alkawari; lafiyayye mai cike da
kuzari; mai saukin kai; mai saurin yafiya; mai kirki; mai son jama’a; mai son zumunci; mai sada alheri tsakanin jama’a; mai yin sallolinsa biyar duka a jam’i;  mai yawan murmushi; mai taimakon jama’a; mai tsayar da addini; mai gaskiya; mai kara; mai hikima; mai hangen nesa; mai fasahar iya zama da mutane; mai wasa da dariya; mai kula da tarbiyyar iyalinsa.; mai kwantaccen hankali; mai wadatar da dukkan bukatun iyalinsa. Mai yawan karatun kur’ani, mai kokarin neman ilmi; mai yawan kyautata zato; mai yawan azumin nafila. Da sauran kyawawan halaye da dabi’un masu kyau abin yabawa.
Za ki iya yaba ma maigidanki ta wadannan hanyoyin: Misali, in Maigidanki ya kasance mai tsananin fada da aiki da gaskiya ne komin tsanani, kuma hakan yana burgeki a cikin zuciyarki; lallai wannan hali ne abin yaba wa duk mai mallakinsa, don haka sai ki samu lokaci mafi dacewa, sannan ki ce da shi
“Maigida gaskiya kullum ina cikin godiyar Allah da ya ba ni miji mai jajircewa wajen rikon gaskiya, kuma ina addu’ar Allah Ya kara karfafa ka ya kare ka daga dukkan aikin rashin gaskiya, amin.” In ma ba za ki iya fada ba sai ki rubuta a takarda ki ba shi ko ki aika masa sakon tes, da sauran su.
Daga cikin wadanda suka yi aiki na farko da aka bayar wancan satin, wata ta fito gaban allo ta labarta mana fa’idar aikata wannan aiki da aka ba ta. “ Da yawan daliban sun daga hannunsu, Bushirah ta bayar da dama ga karamar ajin gaba daya, wacce da alama sabuwar amarya ce mai suna Asma’u ta fito gaban allo cike da kunya tana rufe fuska duk da cewa da nikab a fuskarta. Sannan ta fara bayani kamar haka:
“Na kasance kafin a yi min aure ina yin dukkan addu’o’ina na adhkar da Sallolin nafiloli da sauran ibadodin karin kusanci ga Ubangiji Azza wa Jallah. Amma tunda aka yi min aure a hankali na daina yin su, da kyar nake samu in yi sallah cikin lokacinta, karatun kurani kuwa bai fi sau daya a sati ba. Saboda ayyukan gida da kula da miji da kiyaye kula da kaina sama da yadda nake yi lokacin ina gida. Amma bayan darasin makon jiya, na yi niyyar sa Allah sama da komi a cikin al’amuran rayuwata. Na yi karfin hali na tashi cikin dare na kai kukana ga Allah a kan Ya taimake ni Ya ba ni ikon sa ayyukan addini sama da kowane aiki a rayuwata. Da gari ya waye na ki zuwa in yi aikin komi sai da na gama dukkan adhkar dina da karatun kur’ani, haka ma da rana da dare, na kan tsayar da dukkan wani aikin gida ko na maigida ko nawa har sai na gama gabatar da ayyukan addini na sannan. Haka na dage na rika yi gaba daya cikin satin nan da ya wuce, kuma Insha Allahu haka nake fata cikin taimakon Allah in rika yi har karshen rayuwata. Wannan Ya kara taimaka mini sosai wajen samun natsuwa da kwanciyar hankali, abin mamaki, sai na ga ayyukan gidan sun fi tsaruwa, kuma sun fi tafiya yadda nake so a yanzu da na sa ayyukan addini  sama da ayyukan gida. Na yi matukar farin cikin kasancewata cikin wannan aji mai albarka, ina addu’ar Allah Ya saka wa masu shirya shi da dukkan alheri na duniya da lahira.  To mun gode ‘yar’ uwa Asmau…
Sai sati na gaba za mu ci gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.