✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabudan Sha’awar Uwargida (I)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin.…

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin.

 

A yau inshaAllah za mu shiga tattaunawa kan mabudan sha’awar uwargida. Hakika na samu dimbin sakonnin ku; daga magidanta masu neman hanyar da za su bi don kunno sha’awar matayensu ya kasance su ma suna cimma biyan bukatar sha’awarsu lokacin ibadar aure, da kuma ‘yan uwa mata masu tambayar yadda za su yi su rika cimma biyan bukatar sha’awar su lokacin ibadar aure da ma masu matsalar rashin motsuwar sha’awar gaba daya. Ina fatan wannan bayani duk zai amsa dukkan tambayoyinku In sha Allah.

Akwai wasu ’yanuwa da suka aiko mini da sakonni su na bayanin matsalarsu ta rashin jin motsuwar shaaawa kwata-kwata a rayuwarsu, kuma sun kwatanta yin amfani da magungunan kayan da’a da hakkin maye, da ma wasu bayanan da suka gabata a cikin wannan fili, amma dai ba su taba jin wani canji ba. Sannan wasu suna korafin irin tsananin zafin da suke sha lokacin ibadar auren, suna dai yi ne don ba mazansu hakkinsu na aure, to ga masu irin wannan matsala, ina ga ya fi dacewa a gare su da su je su ga likitan mata (gynecologist) domin watakila akwai wata matsala can kasa da ke haifar masu da wannan rashin jin motsuwar sha‘awa wanda bincike da gwaje gwajen likitoci ne kadai zai iya bayyana hakan.

Sai kuma wasu ‘yan uwa na mata masu korafin yadda mazansu suke masu hawan kawara ba tare da wasannin soyayya da abubuwan kyautatawa da jin dadi a gare su ba, alhali su suna son su rika yi masu wasannin, kuma sun kwatanta ma mazan nasu bukatarsu amma sai su share su, ba su damuwa balle har su yi wani kokarin don ganin cewa su ma sun cimma biyan bukatar sha’awarsu. Yana da kyau magidanta su gane cewa kamar yadda suke yin ibadar aure don irin dadin da hakan ke haifar masu, to sai fa mutum ya so ma dan uwan sa abin da yake son wa kansa; kuma ku yi tunanin in ku ne ake wa irin haka ba za ku so ba kuma ba za ku dauka ba. Sannan ita mace dole sai ta ji dadi, hankalin ta ya kwanta sannan ne sha’awar ta ke iya motsowa, to yaushe sha’awar ta za ta motso tana cikin jin haushin mijinta saboda halin ko in kularsa game da sha‘awarta? Akalla koda ba kullum ba, ko sau 1 ne a sati, sati biyu, ko a duk wata sai maigida ya ware rana daya don jiyar da uwargidansa da kayatar da ita don ganin ita ma ta cimma biyan bukatar sha’awar ta.

Mabudi Na Farko: Uwargida, Gaba dayanta!

Ga Uwargidar da ba ta jin motsuwar sha’awa, ko sha’awar ta na daukar lokaci mai tsawo kan ta motso, ko wacce ke jin sha’awar amma kuma cimma biyan bukatar sha’awa ya yi ta sullube mata, yana kyau ta sani, ita kan ita ce babban mabudin sha’awarta! Ke ‘yar’uwa, ke gaba dayanki, zuciya, ruhi da jikinki su ne babban mabudin sha’awar ki.

Gaba dayan mu jinsin dan adam yanayin halittar mu iri daya ne, ba abin da Allah Ya ba wata macen da bai ba wata ba a halicce, misali, in mun tuna da yadda sha’anin motsuwar sha’awa take, mun san cewa aikin kwakwalwa da sinadaran rai ne ke sa jin motsuwar sha’awa cikin jiki, to akwai macen da Allah Ya halitta ba da cikakkiyar kwakwalwa ba? Ko akwai wacce ba ta da wadannan sinadaran rayin da suke motso da sha’awa? to me ya sa wasu ke jin sha’awar wasu ba su ji?

Amsar ita ce saboda ita kwakwalwa dole sai ta samu wani makunni daga zuciya ko ruhin mutum wanda zai zaburar da ita ta kunna sha’awar har jiki duka ya dumama da sha’awa, to ta yadda wasu suka banbanta da wasu cikin mata ke nan: wasu makunni sha’awarsu mai sauki ne shi ya sa nan da nan sha’awarsu ta kunno, wasu kuma makullin nasu mai wahala ne, a dalilin wasu abubuwa kamar yanayin tasowa; irin al’ummar da aka girma cikinta, wasu al’amura da suka gabata a rayuwa, da yanayin shau’ukan da ke kai kawo cikin zuciya da ma’aikatar hankali duk suna iya sa mutum ya danne makunnin sha’awarsa ya kasance ko ya ya so ya kunno ta ba za ta kunno ba har ta kai shi ya rika tunanin bai da lafiya ta fannin sha’awa alhali lafiyarsa lau.

Ga uwargida da makunnin sha’awar ta ke mata wuyar kunnawa, sha’awarta ba ta dumama ko habaka da wuri, kuma ya kasance haka din yana damunta, tana jin tana son ta gano makunnin sha’awar ta, to sai ta bi bayanin mai zuwa sati na gaba dalla-dalla a aikace. Ga wadda kuwa ke da irin wannan matsala, kuma ya kasance abin bai damun ta kuma bai daga mata hankali, to sai ta kara kwantar da hankalinta, ta yi zaman ta lafiya, domin yadda binciken masana kimiyya ta wannan fannin ya nuna, mafi yawancin mata, su ji dumin mazajen aurensu kusa da su, runguma, sumba da ‘yan wasanni kadan ya wadatar da su ba sai an yi ainihin ibadar auren ba.

 

Zan dakata a nan, sai sati na gaba in Allah Ya kai mu, da addu‘ar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.