Sunnah ta 2: Iya nuna soyayya salo-salo, ci gaba daga makon jiya.
*Sannan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance mai lura da yanayin da matanSs (Radiyallahu Anhun) suke ciki ne a koyaushe, kuma yakan yi hanzarin saka su cikin nishadi duk lokacin da ya lura ba walwala a tare da su, har wata rana ya ce da Uwar Muminai A’isha (Radiyallahu Anha) ta zo su yi tsere don ta wattsake daga rashin walwalar da ya ga ta shiga. Haka kuma a cikin halin tafiya, a gaban jama’a ya rika rarrashin matarsa Ummuna Safiyya (Radhiyallahu Anha) tare da share mata hawaye lokacin da take kuka saboda wani dalili.
Sunnah ta 3: Faranta musu rai; ji da su da kuma shagwaba su:
Annabinmu (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance kwararre, kuma gwani wajen jiyar da matanshi dadi; ya kasance mai kokarin faranta masu rai a koyaushe, kuma yana jiyar da su dadi ta kowace fuska ta rayuwar aure. Domin ya san yanayin halittarsu da halayyarsu da irin abin da suka fi so da irin abin da ya fi kayatar da su. Ya san cewa kirki, da kyautatawa da magana mai dadi da nuna kyakykyawar zamantakewa tafi tasiri da jiyar da su dadi sama da kayan kyale-kyalen rayuwar duniya. Kuma kamar yadda na sha fada, wannan jin dadi shi ne babban mabudin sha’awar ’ya mace.
*Don jiyar da su dadi, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yakan yi wa matansa lakabi da wani suna na musamman, na karramawa sannan mai dadin fada, wanda shi ne kadai ke kiransu da shi. Ya kasance yakan kira Ummuna A’isha (Radiyallahu Anha) da sunan Humaira wanda ma’anarsa ta karramawa ce da yabo gare ta. Wata rana, kuma ya ce da ita “Ya A’ish! Mala’ika Jibril na gaisuwa a gare ki!” Ummuna A’isha (Radiyallahu Anha) ta ce na rasa wanne ya fi min dadi: Shin kirana da A’ish, ko kuwa gaisuwar Mala’ika Jibril?”
*Haka kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance mai yawan sumbatar matansa, saboda mahimmancin hakan, ko bayan ya yi alwalla ne ko yana cikin azumi zai sumbace su, kuma koda lokacin hailarsu ne; musamman duk lokacin da zai fita daga gida. Wannan ma wata kayatacciyar Sunnah ce da malam Bahaushe ya kamata ya yi kokarin rayawa cikin rayuwar aurensa.
*Shin ka taba tsere da matarka? Ko wasan buya? Ko o-diyo-diyo? Da sauran wasanni makamantan wadannan? Ummuna A’isha (Radiyallahu Anha) ta ba mu labarin yadda Annabi (SAW) ya bukaci su yi tsere ita da shi har sau biyu: Na farko ta tsere masa, na biyun kuma ya tsere mata, yana dariya ya ce da ita ya rama waccan tsere masa da ta yi. To ’yan uwa kun ga dai shi (SAW) Manzon Allah ne, Cikamakin Annabawa; wanda nauyin isar da sakon Allah (SWT) ke bisa kansa, amma kuma yana dibar lokaci musamman don yin wasa da nishadantar da matansa! Wani mijin zamanin nan ko hirar kirki bai iya yi da matarsa balle har ya yi wani wasa makamancin wannan da ita. Don haka maigidan da bai taba raya wannan Sunnah ba, sai a yi gaggawa a kokarta yin ta koda sau biyun ne ma don kada a yi rashin dimbin lada da riba ribi-ribi da ke ciki!
Sunnah ta 4: Bayyana darajawa da girmamawa gare su (Radiyallahu Anhun):
*Wannan babban al’amari ne da ya yi karanci a cikin auratayyar mutanen zamanin nan, yawanci ba su daraja juna, wadansu kuma ko akwai darajawar cikin zuciya sai boyeta ba a bayyanawa wai don gudun raini. Magidanta ku sani, daraja mace da bayyana mata ta hanyar girmamawa Sunnah ce da ya kamata ku dabbakar da ita don karin more rayuwar aure.
In muka bibiyi tarihin fiyayyen halitta (Sallallahu Alaihi Wasallam), za mu samu misalai masu dimbin yawa kan yadda yake nuna darajtawa da girmamawa ga matansa (Radiyallahu Anhunna), kuma zai yi wuya ka samu koda wuri daya da ya hulda ce su da akasin haka. Babban misali shi ne yana neman shawararsu kuma ya zartar da abin da suka ba shi shawara, ba ya kaurarawa ko munana kalami a gare su. Yakan duka ya ba su gwiwarsa su taka su hau bisa rakumi, da sauran misalai makamantan haka. Don haka ba ya daga cikin Sunnah maigida ya rika jiji da kai da nuna dagawa ga uwargida ko ya huldace ta ta hanyar nuna mata ita kaskantacciya ce, ko ita mai raunin hankali ce ko kuma ya mai da ita kamar baiwarsa. Da fatan Allah Ya ba dukan ma’aurata ikon dabbakar da sunnonin magidantaka cikin rayuwar aurensu, amin.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.