Rundunar ’yan sandan Najeriya reshen Jihar Ogun ta kama wasu ma’aurata bisa zargin sayar da jaririnsu dan wata daya a kan Naira dubu 50.
Ma’auratan Eze Onyebuchi da kuma matarsa Oluchi Eze, a cewar sanarwar da jami’in yada labarai na rundunar Oyeyemi ya fitar, ma’auratan suna zaune ne a Unguwar Ilara da ke Ode Remo, a Karamar Hukumar Remo ta Arewa a Jihar Ogun.
- An ayyana makokin kwanaki 2 bayan kashe mutum 41 a Burkina Faso
- Mafarauta sun yi wa ’yan bindiga kwanton bauna, sun ceto mutum 9 a Kaduna
Oyeyemi ya ce, “An kama wadanda ake zargin ne a ranar 16 ga Disamba 2021, biyo bayan bayanan da ’yan sanda suka samu a hedikwatar Ode Remo, cewa ma’auratan da ke zaune a titin Ayegbami, Lara Remo sun sayar da jaririnsu dan wata daya ga wata mata da yardar maigidanta ne wanda a halin yanzu ya zo ofishin.”
Da samun wannan labarin, shugaban ofishin ’yan sanda na garin Ode Remo (DPO) CSP Olayemi Fagbohun, ya yi karin bayani ga jami’an bincikensa a yankin da aka kama ma’auratan aka kawo ofishin.
Da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun bayyana wa ’yan sanda cewa, Misis Ruth Obajimi ce ta umurci wanda ya saya masu jaririn.
Sun kara da cewa matar ta zo musu ne a ranar 14 ga watan Disamba 2021, kuma ta shaida musu cewa, ta fito daga ofishin kare hakkin bil’adama kuma za ta taimaka musu wajen renon ’ya’yansu.
Daga bisani, matar da ta sayi jaririn ta ba su Naira dubu 50 suka mika jariri a gareta duk da cewa, mijin matar bai san an kammala cinikin ba. Oyeyemi ya kara da cewa, ana kokarin damke wannan matar da nufin kwato jaririyar.
A halin yanzu, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Lanre Bankole ya bayar da umarnin mika wadanda ake zargin cikin gaugawa ga sashin yaki da fataucin bil Adama da aikin sa yara aikatau na sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar, domin ci gaba da bincike.
Haka kuma ya ba da umarnin farautar mai saye wanda tun a lokacin ya tashi.