✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa Kafin Ramadan

1. Kyauatata Niyya: Abu na farko, kuma mafi alfanu, shi ne ma’aurata su daura kyakykyawar niyyar cin ribar wannan muhimmin lokaci don dacewa da dukkan…

1. Kyauatata Niyya: Abu na farko, kuma mafi alfanu, shi ne ma’aurata su daura kyakykyawar niyyar cin ribar wannan muhimmin lokaci don dacewa da dukkan alheran da ke cikinsa. Za su yi haka ne ta hanyar kudurta wa ransu dagewa wajen yin dukkan ayyukan ibada da na kyautatawa don su samu dacewa da rahma da gafarar da Allah Ya yi tanadi ga bayinSa da suka aikata kyawawan ayyuka a cikin wannan wata. Haka kuma in ma’aurata suka kudurta wa kansu yin ayyukan alheri cikin wannan wata, wannan zai kara masu taushin zuciya ya kuma bude masu hanyar karuwar imani. Kamar yadda Annabi (SAW) Ya sanar mana cewa dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, don haka duk wani aikin da ma’aurata ke son aiwatar da shi cikin Ramadan, to sai su fara da kulla masa kyakykywar niyya tun yanzu, kuma su tabbatar da niyyar nan cikin zuciyarsu, sannan kullum su yi ta kara jaddada wa kansu wannan niyya, koda ta hanyar rubutawa a takarda don karantawa kullum har sai wannan niyya ta zama babba kuma sanannen kudiri cikin zuciyarsu, wannan zai zama garanti gare su na cewa lallai in Ramadan ya tsaya, to za su samu nasarar aiwatar da dukkan ayyukan alherin da suka yi niyya. Haka kuma ma’aurata suna iya rubuta kudurorin da suke son cimma aiwatar da su cikin Ramadan a takarda, tare ko daban-daban, sai su rika  karantasu don jaddada su cikin ma’aikatar hankalinsu.
2. Shirya Zuciya: Ta hanyar yawan karanta Ayoyin kur’ani safe da maraice, yin kyakykyawan tuba ga laifukan da mutum ya aikata; yawan kyauta da yin sadaka ga mabukata; gyara zuciya da kawatata da ayyuka masu kyau, raya ta da yawan tunanin Allah da kyautata zato gareShi da kuma guje wa aikata ayyukan sabon Allah da munana zato ga Allah SWT, duk ayyukan dake kusanta bawa ga Ubangijinsa ne wadanda tun kafin Ramadan yakamata a fara gabatar da su ba lallai sai cikin Ramadan kadai ba, zuciyar mu’mini mai bukatar Ubangijintane a kowane lokaci.
3. Shirya Muhalli: Babban bako, mai matukar muhimmanci zai bakunci gidanku ya ku ma’aurata; don haka yana da matukar muhimmanci ku yi dukkan shirin da yakamata don yi masa tarba mai kyau da ba shi mafi kyawun masauki a cikin gidanku. Don tabbatar da haka, sai ku yi amfani da wadannan hanyoyi:
· Kwana biyu ko uku kafin Ramadan, sai a share gida gabadayansa, a cire yana, a kwashe kwata; a rage tarkace, mai sauran amfani a kyautar ga masu bukata, marasa amfani a zubar a bola; sannan a rage like-like da kayan kawa, musamman hotuna da like-liken kwalliya masu daukar hankali lokacin ibada; sannan a gyara wuraren da siminti ya farfashe musamman in ruwa na yawan taruwa a wurin; in kuma fentin gidan ya tsufa, kuma inda halin yin sabo to sai a yi ga duka ko wani bangare mafi muhimmanci na gidan.
· A tanadi hanyar samun ruwan amfanin yau da kullum, kuma a tanadi hanyoyin samun haske da daddare.
· A tabbatar cewa murhun da ake amfani  da shi, na itace, risho ko na gas, bai da wata matsala, in kuma yana da matsala a yi kokarin gyarawa kafin Ramadan. Sannan a tanadi makamashin konawa, watau itace, kalanzir ko gas daidai gwargwadon hali.
· A tanadi dukkan kayan abinci daidai gwargwadon hali, sannan masu bukatar gyara sai a gyara su yadda da an zo amfani da su cikin Ramadan, kawai sai dai a sarrafa ba sai an tsaya gyarawa ba.
· A yi dukkan saye-sayen kayan Sallah, da dinkunan Sallah tun kafin Ramadan, ta yadda in watan ya tsaya sai dai a maida hankali wajen ibada da bautar Allah kadai.
· A kaurace wa kallon talabijin ko sauraren kide-kide, sai na shirye-shiryen Addini kadai; in kuma har ya kasance garin kallonsu za a kunno wasu tashoshin wasannin banza, to sai a dauke talabijin din gaba daya daga wajen kallon har sai bayan Ramadan.
4. Jadawalin Ramadan: Lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar bil’adama, rashin sarrafa shi yadda ya kamata na jawo wa dan’adam asara mai yawa da kuma ci baya a rayuwarsa. Don haka duk mai son ya ribaci dukkan alheran da ke cikin watan Ramadan, dole sai ya tsara, ya kuma shirya lokacinsa ta hanyar yin abubuwan da suka dace a lokacin da suka dace. Abin da zai taimaka wa mutum cimma wannan shi ne ta hanyar yin jadawalin lokacinsa. Yin jadawali da amfani da shi abu ne mai matukar muhimmanci kuma mai tabbatar da cin nasara cikin rayuwa.
Yadda za a tsara Jadawalin Ramadan: Don samun sauki wajen tsarawa, sai ma’aurata su tsara ayyukan da suke son aiwatarwa  a rana a cikin sa’o’in dake tsakanin lokacin sallolin farilla biyar; misali, sai a fara da ayyukan da ake son aiwatarwa a lokacin sahur, bayan Sallar Asuba kafin Sallar Azahar; bayan Azahar kafin la’asar; bayan la’asar kafin magriba; bayan magriba kafin isha’i; bayan isha’i da tarawiy kafin lokacin sahur; sai a bi a cike wadannan lokuta da ayyukan da suka dace, kuma ana fara sa aikin da ya fi muhimmanci, ko wanda yake dole, sannan mai bi masa a muhimmanci, sannan mai bi masa har a hada duka. Tunda ba komai ne ma’aurata ke yi tare ba, kuma ba kodayaushe suke tare ba, yakamata ma’aurata sun kasance kowa yana da jadawalinsa, sannan kuma su yi wani na gida guda daya wanda zai kunshi kowa da kowa har yara duka. Don ganin alfanun da ke cikin yin jadawalin lokaci, DOLE sai ma’aurata sun ladabtar da kansu ga yin amfani da shi yadda yake, ba tare da tsallake wani aiki ba ko daukar aikin wani lokaci a kai shi wani lokaci, kuma dole su ladabtar da dukkan wadanda ke karkashinsu wajen yin aiki da jadawalin nan sau da kafa.
5. Gyara Dangantaka: Ma’aurata, yana da kyau ku yi dukkan kokari na gyara da inganta dangantakarku kafin isowar watan Ramadan, da haka ne za ku dace da cin ribar dukkan alheran da ke cikinsa. Ku yi kokarin kara kusanci da shakuwa da juna, da kuma kara karfafa zumuncin auren da ke tsakaninku. karin kyautatawa ga juna, karin yin hakuri da juna, da sauran kyawawan abubuwa na dadada wa juna. Ku zauna ku tattauna game da dangantakarku, ku yi afuwa ga juna, ku toshe duk wata baraka da ke tsakaninku don ya kasance in Ramadan ya zo, ba abin da ke gabanku sai more rahamar da ke cikinsa da yin ibada.