Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Ga bayani mai kunshe da kyawawan ayyukan da yakamata ma’aurata su dage gabatarwa don dacewa da dimbin alheran dake cikin wannan wata na Ramadan, da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkanin alheran da ke cikin wannan wata, amin
1. Dagewa da Addu’a:
Ya ’yan’uwana ma’aurata! Mu sani fa wannan wata ne na amsar addu’a da karbar tuba, dukkanmu muna da dimbim bukatun da ba za su kirgu ba, kuma dukkaninmu masu laifuka ne da ba mu san iyakarsu ba, don haka kada mu yi sanya; yana da matukar alfanu garemu da mu zauna mu rubuta dukkan bukatunmu gabadaya a takarda, ya kasance in mun zo yin addu’a sai mu dauko mu karantasu ta haka ba za mu mance da ko daya ba daga cikin bukatunmu. Da fatan Allah Ya amsa mana dukkan addu’o’inmu, kuma ya sa mu dace da dukkan alherai da albarkokin wannan wata na Ramadan, amin.
2. Yin hakuri da iyali:
Musamman yara; sai a daure kar a rika yi masu tsawa ko yi masu fada cikin fushi. A yi masu magana cikin hakuri da lallashi. Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallam yana cewa: “In dayanku na azumi, sai ya guji yin mummunar magana da kace-nace; in kuma wani ya neme shi da fada, sai ya ce da shi ni ina azumi.” Don haka ma’aurata a dage da yin hakuri da juna cikin wannan wata, maigida ya yi hakuri kar ya yi fushi da uwargida don ba ta gama abincin buda baki da wuri ba, kada kuma ya matsa mata da dole sai ta girka sabon abinci lokacin sahur.
3. Yin kiyamullaili tare da yara duka:
Ummuna Aisha RA ta ce in goman karshe na Ramadan ya zo, Annabi SAW Yana raya dare gabadayansa, sannan zai tayar da iyalansa su ma don su raya dare. Don haka sai ma’aurata su dage wajen yin koyi da wannan kyakykyawar Sunnah ta Annabinmu SAW; sai a riki dabi’ar sa yara su yi barci da wuri don tashi tsakar dare yayi masu sauki sosai. Kuma Maigida na iya sa wata ‘yar kyauta ga duk wanda ya dage daga cikin yaransa wajen yin kiyamul laili da karatun Alkurani don hakan zai su kara dagewa sosai. Da fatan Allah Ya yi mana gam-da-katar mu zama daga cikin wadanda za su raya dukkan dararen watan Ramadana da kyawawan ibadoji, amin.
4. Yin Ayyukan Sabunta Imani Tare:
· Gabatar da Sallar kiyamul laili tare cikin kowane dare; da kuma yin addu’o’in neman biyan bukatunsu cikin wannan dare tare; maigida na rokawa uwargida na cewa amin, ko su rika roka wa tare.
· Yin addu’o’in neman tsari na safe da yamma tare.
· Ma’aurata su zauna kusa da kusa, hannun uwargida rike cikin hannun maigida, yayin da suke karatun Alkur’ani mai Tsarki tare, ko sauraren karatun ayoyinSa, ko daya na karantawa dayan na saurare, ko su saurari tafsirin ma’anonin ayoyinSa tare, da yin haddar wani bangare na Ayoyin Al-kur’ani tare.
· Yin musaffar karatun kur’ani Mai girma tare, watau kamar in maigida ya karanta Ayar farko Uwargida sai ta karanta Ayar da ke biye, in ma mata biyu ne uku ko hudu, duk sai a hadu a yi tare, ana kuma iya yi har da yara duka. Wannan ya fi a zauna a yi ta kallon fina-finai da sauran shirye-shiryen talabijin marasa alfanu, kuma wannan ya fi kayatarwa da sa nishadi cikin zuciya, duk wanda ya ji ya karanta wata aya da gargada, ko ya kasa kawo ta ma gabadaya, to zai dage ya je ya koye ta ya ga ya iya ta.
To me ya fi wannan dadi? Mutum yana tuna Ubangijinsa tare da mafi kusanci gare shi daga cikin mutane, Mala’ikun Rahma za su sauka a lokacin su lullube ku da rahma, suna sa maku albarka suna roka maku gafara, maimakon kallon fina-finai da shaydanu ne ke zama su taya ku kallon, da fatan dukkan ma’aurata za su maye dukkan wani kallon da suka saba yi, in banda na tafsir da sauran abubuwan fadakarwa da musaffar karatun kur’ani mai Girma, ko wata ibada sassauka, amin; domin gara ma a zauna ayi hira cikin raha da irin wannan kallace-kallacen
Sai sati nag aba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.
Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan
Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin.…