Wani bincike da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa na’urar tauraron dan adam guda uku na miliyoyin Dala mallakar kasar Najeriya na yawo a sararin samaniya ba tare da samarwa kasar kudin shiga na azo-a-gani ba.
Kasar ta kaddamar da tauraron dan adam dinta don ta samar da sadarwa da hotuna da kafar yanar gizo ga hukumomin gwamnati da kuma ma’aikatu masu zaman kansu.
Kasar ta yi tsammanin kaddamar da tauraron dan adam din da ta yi zai ceto kasar daga biliyoyin kudin kasashen waje da take kashewa tare da samar da kudin shiga masu yawa ga gwamnati.
Jami’ai da masana da kwararru kan sararin samaniya sun fada wa Aminiya cewa da yawa daga cikin hukumomin gwamnatin sun ci gaba da yin amfani da tararon dan adam na kasashen waje sakamakon haka kasar ta rasa kudin shiga kimanin Dala biliyan 20 kwatankwacin Naira biliyan 720 a duk shekara.