✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatar lafiya ta tabbatar da bullar cutar Kurona a Legas

Cutar nan mai kisa a China ta bulla a Jihar Legas, ma’aikatar lafiya ce ta tabbatar da bullar cutar, a wata sanarwa da tayi a…

Cutar nan mai kisa a China ta bulla a Jihar Legas, ma’aikatar lafiya ce ta tabbatar da bullar cutar, a wata sanarwa da tayi a shafinta na tweeter a ranar Juma’a.

Haka zalika, a sanarwar da Ministan kiwon lafiya a Najeriya Dakta Osagie Ehanire, ya bada sanarwar an sami wani mutum dan kasar Italiya dauke da cutar wanda ya shigo Legas daga birnin Milan, ya ce sakamakon gwajin da aka gudanar akan mutumin a jami’ar Legas ya tabbatar da mutumin na dauke da cutar.

Kana zuwa yanzu ana kula da lafiyarsa a asibitin kula da cututtuka masu yaduwa da ke Yaba a Legas, kuma mutumin bai nuna alamu mai muni ba.

A yanzu dai Najeriya ta shiga jerin kasashen Afirka biyu da suka tabbatar da bullar cutar Kurona, inda ta zamo ta uku a jerin kasashen da cutar ta bulla bayan kasa Masar da Aljeriya.