✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan Zariya 9 sun kubuta bayan biyan fansar N40m

A yanzu 'yan bindigar suna bukatar sabbin babura biyu kafin sakin sauran ma'aikatan.

Mutum 9 daga cikin Ma’aikata 11 na Karamar Hukumar Giwa da ke garin Zariya da aka yi garkuwa da su sun kubuta bayan shafe kwanaki 19 a hannun ’yan bindigar da ke tsare da su.

Wadanda suka shaki iskar ’yanci su 9 da suka kasance mata, sai da aka biya kudin fansa na Naira miliyan 40 gabanin sakinsu.

Majiyoyi daga ’yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su sun ce ’yan bindigar sun bukaci sabbin babura biyu a matsayin fansar da za ta su sako ragowar mazan biyu da ke hannunsu.

Da yake zanta wa da wakilinmu, dan uwan wata daga cikin wadanda aka sako, ya ce da fari ’yan bindigar sun bukaci kudin ne da kuma sabbin baburan biyu.

Amma daga bisani suka sako matan suka ci gaba da rike mazan biyu har sai an kai musu baburan.

Aminiya ta ruwaito cewa, kusan makonni uku ke nan  suka fada tarkon wasu ’yan daban daji da suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ce aka yi garkuwa da mutanen wadanda Ma’aikatan Karamar Hukumar ta Zariya ce a kan hayarsu ta zuwa ta’aziyar mahaifin wani abokin aikinsu a kauyen Idasu.

Bayanai sun ce batan hanya ya sanya Ma’aikatan suka nemi wani da ke haye a kan babur da ya yi musu kwatance, ashe abun nema ne ya samu kasancewar mutumin da suka nemi taimakonsa dan koran masu garkuwa da mutanen ne.

A halin yanzu dai matan 9 da suka kubuta an garzaya da su wani asibiti da ba a fayyace sunansa ba inda ake bincike domin tabbatar da ingancin lafiyarsu.