Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta ce mambobinta za su bi sahun ragowar ’yan kwadago wajen shiga yajin aiki saboda janye tallafin man fetur.
A makon da ya gabata ne dai Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da karin kudin mai zuwa sama da N500, bayan Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man.
- ’Yan bindiga sun kashe manoma 2 a Kaduna saboda kin biyansu ‘haraji’
- An kashe mutum 2 a rikicin sojoji da matasa a Jos
Ko a karshen makon da ya gabata sai da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta sanar da fara yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa.
Kazalika, ita ma JUSUN, a cikin wata sanarwa ta bakin Babban Sakatarenta na Kasa, M.J. Akwashiki, kungiyar ta umarci dukkan rassanta da ke jihohi da su fara yajin aikin daga ranar Laraba.
“Daukar matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwar Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), a taronta na ranar 2 ga watan Yunin 2023 saboda karin kudin man da Gwamnatin Tarayya ta yi ta hannun NNPCL,” in ji shi.
Ya kuma ce Mataimakan Shugaban Kungiyar na shiyyoyi su tabbatar mambobinsu sun bi umarnin sau da kafa.