✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 2 a rikicin sojoji da matasa a Jos

Lamarin ya faru ne lokacin da matasan ke kokarin zuwa jana'iza

An kashe mutum biyu, wani kuma na can an ji masa mummunan rauni bayan wasu matasa sun yi taho-mu-gama da sojoji a wajen wanu shingen jami’an tsaro da ke Maraban Jema’a, a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Lamarin wanda ya faru ranar Litinin ya jefa mummunan tsoro inda mazauna yankin suka rika gudun neman tsira.

Kazalika, matafiya sun kaurace wa babbar hanyar Maraban Jema’a zuwa Marabar Zerwan, wacce take kai wa ga birnin Jos.

Rikicin ya fara ne lokacin da wasu masu jimami suke dawowa daga dakine ajiye gawarwaki da wata gawa zuwa wajen birne ta, inda suka wuce ta shingen.

Bayanai sun nuna cewa lokacin da matasa masu jimamin suka je wuce shingen a kan babura, sai sojojin suka bukace su da su sauka su tura.

To amma sai dai matasan sun ki bin umarnin sojojin, inda a madadin haka, suka bukaci a kyale su, tun da wajen jana’iza za su je.

Sai dai bayan tsawon lokaci ana ta cece-ku-ce, sai aka kasa cim ma matsaya tsakanin bangarorin biyu, daga bisani kuma aka ji karar harbe-harbe a sama.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa a sakamakon taho-mu-gamar, an harbi matasa uku, inda daya ya mutu nan take, daya kuma a asibiti, yayin da wasu biyu kuma aka garzaya da su asibiti.

Majiyar ta ce sakamakon fusatar da matasan suka yi da hakan, sai suka fara zanga-zanga sannan suka kone motar sojojin.

Amma da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH), Kyaftin John James kan lamarin, bai amsa kiran waya da rubutaccen sakon da aka aike masa ba.

Sai dai wakilinmu ya gano cewa yanzu haka mata na can suna kokarin shirya wani gangamin zanga-zanga a kan babbar hanyar yankin.