Ma’aikatan Shari’a na Babbar Kotun Tarayya da ke fadin Najeriya, sun bayyana aniyyarsu ta shiga yajin aiki na makonni biyu wanda zai fara daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.
Cikin wata sanarwa da Ma’aikatan karkashin kungiyarsu mai suna JUSUN suka fitar, za su shiga yajin aikin domin yin biyayya ga umarnin kungiyar kwadago na shiga yakin aiki a farkon makon gobe.
Kungiyar Kwadago NLC da takwarta ta ma’aikata TUC, sun sanar da cewa za su shiga yajin aikin idan har Gwamnatin Tarayya ba ta janye karin kudin wutar lantarki da na man fetur da ta yi ba.
Shugaban JUSUN, Marwan Adamu, yayin zanta wa da manema labarai na jaridar The Punch, ya ce kasancewarsu a karkashin kungiyar kwadago ta NLC, za su bi sahunta na fara yajin aikin daga ranar Litinin.
“Wannan yajin aikin ba na kungiyar JUSUN bane, na NLC ne.”
A matsayinmu na mambobi a karkashin NLC dole mu yi biyayya ga umurninta don haka za mu shiga yajin aikin,” in ji Adamu.