Ma’aikatan Hukumar Kula da Shaidar Zama Dan Kasa (NIMC) sun janye yajin aikinsu wanda ya kawo tsaiko ga rajistar da ’yan Najeriya ke tururuwar yi.
A ranar Juma’a suka janye yajin aikin gargadin da suka shiga ranar Alhamis, kamar yadda Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN) reshen NIMC ta shaida wa wakilinmu.
- Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba
- Dalilin da na ziyarci Fulanin hanyar Kaduna zuwa Abuja —Dokta Gumi
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
- An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina
Shugaban Reshen, Lucky Michael Asekokhai ya ce, “Mun janye yajin aikin kuma duk ’yan kungiyarmu za su koma bakin aiki ranar Litinin.”
Ya ce kungiyar ta cimma burinta da yajin aikin na kwana sannan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya bukatun ma’aikatan a kan lokaci ko kuma ta kuka da kanta.
Za mu koma yajin aiki idan…
Kungiyar ta ba wa Gwamnatin sabon wa’adin kwana 21 ta biya bukatun ma’aikatan ko kuma su shiga wani yajin aikin.
A ranar Talata ake sa ran Gwamnati za ta tattauna da wakilan ma’aikatan NIMC a Abuja game da bukatunsu da kuma jin dadinsu.
Wani babban jami’i a Hukumar ya ce Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, wanda hukumar ke karkashin ma’aikatarsa, shi ne zai jagoranci bangaren gwamnati a tattaunawar.
Shugabannin Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikata ta TUC ma za su halarci zaman, inji jami’in wanda ya bukaci a boye sunansa.
Idan ba a manta ba ma’aikatan sun tsunduma yajin aiki ne domin neman gwamnati a fara biyan su da sabon tsarin albashi, sai kuma batun kariyarsu daga COVID-19 a yayin rajistar shaidar zama dan kasa.
Yayin aikin ya kawo tarnaki a aikin rajistsar wadda jama’a ke rige-rigen yi bayan da gwamnati ta ba da umarnin rufe layukan waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar dan kasa ta NIN ba.