✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan lafiya na yajin aiki duk da barazanar kora

Ma’aikatan lafiya sun shiga yajin duk da barazanar da gwamantin jihar Kaduna ta yi na sallamar duk wanda ya ki zuwa wurin aikinsa. Yajin aikin…

Ma’aikatan lafiya sun shiga yajin duk da barazanar da gwamantin jihar Kaduna ta yi na sallamar duk wanda ya ki zuwa wurin aikinsa.

Yajin aikin na kwana bakwai na zuwa ne bayan hadaddiyar kungiyar ma’aikatan lafiya (HCWS) ta zargi gwamantin jihar da kin dakatar da zabtare kashi 25 na albashin ‘ya’yanta da kuma kin ba su kayan kariya a yakin da suke yi da annobar coronavirus.

Gwamnatin jihar ta fara cirar kashi 25 na albashin ma’aikatanta da kuma rabin albashin ‘yan siyasa ne domin sayen kayan tallafi ga matalauta da raunana a lokacin dokar kullen da ta sanya domin dakile yaduwar cutar.

Barazarar kora daga aiki

Bayan gargadin shiga yajin aikin kungiyar, gwamnatin jihar ta ce duk ma’aikacin lafiyar da bai je wurin aikinsa ba to ya sallami kansa.

A cikin wata sanarwa , mai ba gwamna Nasir El-Rufa’i shawara kan yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya umurci ma’aikatan lafiyan da ke son ci gaba da aikinsu su sanya hannu a rijista idan su je aiki a cibiyoyin lafiyar da suke aiki.

 

Martanin ma’aikatan lafiya

A martaninta kungiyar HCWS ta ce ta shiga yajin aikin gargadin ne saboda gwamnatin jihar ta ki sauraran bukatun ‘ya’yanta da ke kan gaba a yaki da cutar coronavirus. Ta kuma ce dibar albashin ‘ya’yanta na watannin Afrilu da Mayu ya saba dokar kwadago.

HCWS ta kuma zargi gwamnatin da biyan alawus din naira 150,000 zuwa 450,000 ga wasu zababbun ma’aikatan lafiya 300 a cibiyoyin kuda da cututtuka masu yaduwa, wuraren killacewa masu cutar coronavirus.

 

Hadarin da ma’ikatan lafiya ke ciki

“Kasa da kasha 2 na ma’aikatan lafiya an biya hakkokinsu, amma har yanzu ba a biya ‘yan HCWS alawus din kashi 10 da aka yi alkawari ba.

“Yawancin ‘yan HCWS da suka kamu da COVID-19 sun harbu ne a wasu cibiyoyin kula da lafiya. A cikinsu babu wanda aka alawus din N100,00 na kwana 10 da aka yi.

“Har yanzu ba a nemi masu aiki a asibitoci su ba da bayanan su na ajiyar banki ba domin biyan alawus dinsu na naira miliyan biyar da miliyan biyu na inshorar rai da gabban jiki ba.”

 

A shirye muke a tattauna

Sanarawar ta ce jami’an lafiya na cikin hadarin kamuwa da cututtukan COVID-19, zazzabin Ebola, zazzabin Lassa, tarin fuka da kuma cutar AIDS. Duk da haka ba a ba su kayan kariya. Marasa lafiya ke sayen safar hannun da ake musu amfani da shi.

Ta ce likitocin na yajin aiki kafin bullar annobar coronavirus a jihar, amma suka dakatar suka koma aiki kuma a shirye suke su tattauna da gwamnati.