Ma’aikata da dama a Jihar Katsina sun koka kan yadda suka ce Gwamnatin Jihar ta zaftare musu albashinsu da nufin taimaka wa ’yan kasuwar da iftila’in gobara a babbar kasuwar Katsina ya afkawa.
Wasu daga cikin ma’aikatan da suka tattauna da Aminiya amma suka nemi a sakaya sunansu sun ce ba su ga dalilin da zai sa a debi albashinsu ba tare da amincewarsu ba.
A ta bakin daya daga cikinsu, “Tun da ake tarihin gobarar kasuwa, ba mu taba jin inda aka debi wani kaso na albashin ma’aikaci don bayar da tallafi ba.
“Shin wane taimako ’yan kasuwar suke bamu? Bashi da ruwa ko kara farashin kaya? Wurare nawa suka yi gobarar a cikin jihar, amma an cire kudinmu don tallafa musu? Haba jama’a! Farko wadanda aka ce za a ba mutanen nan sun ce ba su so.”
Shi kuwa wani da aka yanke wa sama da N5,000, cewa ya yi, “Inda ma wadanda aka raba da muhallansu, iyayen su ko danginsu, ina nufin wadanda ’yan bindigar daji ke kashewa, aka ce za a ba wallahi da bamu damu ba.
“Amma ai su wadannan ’yan kasuwa tuni wasun su suka fara gane kura-kurakunsu na kin fitar da hakkin Allah da kuma gauraya dukiyarsu da haram, tuni suka fara neman hanyar tuba.
“Ai mun ga yadda shagon wani bawan Allah ya tsira, sannan mun ga yadda aka dauki dukiyar aka sanya cikin masallaci gobarar ta bi ta har can bayan farko gobarar ta tsallake masallacin.
“Har gidan sarki sun je don nuna rashin amincewarsu da cire kudaden, amma sai ga shi an cire.
“Kusan mafi yawan ma’aikatan wadanda baya ga bacin rai na rashin biyan su albashin akan lokaci har sai da wani watan ya kama, sannan kuma sai gashi an cire musu kashi uku cikin 100 na albashin,” inji shi.
Matsayar Gwamnatin Katsina kafin zaftare albashin
Tun da farko dai gwamnatin jihar ta ce zata yanki wani kaso na albashin ma’aikatan don tallafawa su ’yan kasuwar da iftala’in gobara ya shafa.
Gwamnatin ta ce sai da ta tuntubi dukkan dukkan masu ruwa da tsaki a kan lamarin tare da samun amincewarsu.
Yanzu dai ma’aikatan sun zura ido don dakon abin da zai biyo baya muddin ’yan kasuwar suka tsaya kai da fata cewar ba sa son tallafin.
A gefe guda kuma, idan suka karba, yaya za a yi a batun hauhawar farashin kaya a kullum.
Har ila yau, wasu kuma na jiran su ga me gwamnatin za ta yi a kan wadanda suka yi asarar fiye da abin da ’yan kasuwar suka yi sanadiyyar iftila’in ’yan bindiga da barayin shanu a Jihar.