✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan jami’o’i za su fara zanga-zanga ranar Talata

Batutuwan da kungiyar take ja da gwamnati a kai sun hada da IPPIS da kudaden alawus

Ma’aikatan jami’a da ba malamai ba a Najeriya sun ce sun kammala shriye-shiryen fara zanga-zanga ta kwanaki uku saboda zargin saba yarjejeniyarsu da Gwamnmatin Tarayya.

Batutuwan da kungiyar take takun saka da gwamantin a kai sun hada tsarin biyan albashin bai-daya na IPPIS, kudaden alawus-alawus na Naira biliyan 40 da kuma kin biyan su basukan mafi karancin albashi da suke bi.

Kungiyoyin, karkashin jagorancin JAC wadanda suka kunshi kungiyoyin SSANU ta manyan malaman jami’a da NASU ta ma’aikatan jami’a da ba malamai ba, tuni suka umarci ’ya’yan da su fara shirin ko-ta-kwana.

Kungiyoyin sun ce sun dauki matakin ne don nuna kin amincewarsu da rashin daidaiton da ake samu a tsarin biyan albashin IPPIS, jan kafar gwamnatin wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a 2009 da sauran batutuwa.

A wata takaradar bayan taro da kungiyoyin suka fitar ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim da Babban Sakataren NASU, Prince Peters Adeyemi sun ce sun yi bitar yarjejeniyar da suka rattaba wa hannu da gwamnatin ranar 20 ga watan Oktoban 2020.

Kungiyoyin sun kuma koka kan rashin biyan kudaden ritaya ga tsofaffin mambobinsu, rashin kafa kwamitocin ziyara zuwa jami’o’i, rashin ba jami’o’in wadatattun kudaden gudanarwa, nuna bambanci da tazara mai yawa tsakanin malamai da sauran ma’aikatan jami’o’i da sauran batutuwa.

JAC ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace, ciki har da yajin aiki da zanga-zanga, domin ganin bukatunsu sun biya.

Kwamitin kungiyoyin zai zauna ranar Alhamis domin tattauna batun zanga-zangar da kuma duba mataki na gaba.

Idan za a iya tunawa, a watan Disamban 2020 ne gwamnatin ta biya Naira biliyan 40 ga kungiyoyin jami’o’in hudu a matsayin kudaden alawus-alawus dinsu.

Sai dai kusan kaso 75 cikin 100 na kudaden za su tafi ne ga Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU), lamarin da bai yi wa sauran kungiyoyin dadi ba har, suke barazanar kassara ayyukan jami’o’in matukar ba a sake kasafta kudaden ba.