Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta bukaci Kananan Hukumomi a jihar Sakkwato da su samar wa da ma’aikatan Kidaya na jihar tsaro.
Wakilin hukumar dake kula da jihar Sakkwato, Alhaji Chuso Abdullahi Dattijo ne ya yi wannan kira yayin da yake rangadi don ganin yadda aikin ke gudana a Karamar Hukumar Binji dake jihar.
- 2023: APC ce za ta lashe zaben Gwamnan Sakkwato —Dingyadi
- COVID 19: Gwamnan Sakkwato yana rokon addu’a
“Amma yana da kyau a ce kananan hukumomi sun samar wa da ma’aikatan tsaro, saboda yadda harkar ta lalace,” in ji sa.
Ya ba da tabbacin cewa dukkan Kananan Hukumomin jihar 23 za a kewaya su tare da tabbatar da an kidaya mutanen cikinsu.
Daga nan ya jinjinawa Karamar Hukumar Tureta da suka samar da jami’an tsaro ga ma’aikatan.
Ya kuma yi kira ga sauran kananan hukumomin da su samar da tsaro a yayin da ake musu aikin.
Chuso, wanda tsohon Mataimakin Gwanan jihar ne, ya bukaci jama’a da su ba da hadin kai ga ma’aikatan wajen shiga gidajensu, domin yin kidayar.
Sannan ya gode wa jami’in dake kula da aikin kan samar da masauki ga ma’aikatan.