Gwamnatin Tarayya ta amince a rika ba wa ma’aikatanta maza hutun kwana 14 idan aka yi musu haihuwa.
Sabon tsarin hutun da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi a zamanta na ranar Laraba ya nuna daga yanzu za a rika lissafa hutun ma’aikata ne da ranakun aiki, sabanin ranakun kwanan wata da ake lissafa a baya.
- El-Rufai ya haramta amfani da babura a Kaduna
- An kama daliban Najeriya kan juyin mulkin kasar Turkiyya
Da take sanar da hakan, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta ce maimakon tsarin da ake bi na jarabawar karin girma, yanzu za a koma auna ingancin aikin ma’aikata.
“Tun shekarar 2008 rabon da a sabunta wadannan tsare-tsaren aikin gwamnati; saboda haka abu ne da lokacin yin sa ya da dade da wucewa,” kuma an yi ne da gudunmawar masu ruwa da tsaki.