✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan filin jirgin Kano sun zargi sojoji da yin gini a gaban gidajensu

Ma’aikatan filin jirgin Kano sun yi zanga-zanga kan ‘ginin da sojoji ke yi a gidajensu’

Maaikatan filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano sun gudanar da zangazangar lumana don nuna rashin gamsuwarsu da wani gini da Rundunar Sojin Sama take yi a gaban gidajensu.

Sojojin dai na yin gine-ginen ne a gaban gidajen nasu da ke rukunin gidajen na ma’aikatan filayen jiragen sama da ke Kano, wato Aviation Quarters.

Shugaban Harkokin Tsaro da Walwalar Ma’aikatan, Kwamared Muhammad Zakariyya Dauda ya ce sun wayi gari sun ga sojojin sun mamaye unguwar tasu tare da yi musu gini a filin da suke motsa jiki su da ’ya’yansu.

“Muna wajen aiki ne ’yan uwanmu da ke gida suka yi mana waya cewa sojoji sun yi mana kutse a gidajenmu tare da fara gini a filin da ke cikin gidajenumu.

“Wannan fili shi ne muke amfani da shi wajen motsa jiki mu da ’ya’yanmu. Ba su tuntube mu ba suka cire mana allon da ke dauke da sunan hukumarmu a jiki.”

Haka kuma ma’aikatan sun zargi sojojin da hana su shiga gidajensu tare da dukan wani daga cikinsu a daidai lokacin da yake kokarin sauke ’ya’yansa da ya dauko daga makaranta.

“Wadannan sojojin sun hana ma’aikatanmu shiga gidajensu har ma suka sa kan bindiga suka doki wani ma’akacinmu a lokacin da yake kokarin shiga unguwar don sauke ’ya’yansa da ya dauko daga makaranta,” in ji Kwamared Muhammad.

Har ila yau, ma’aikatan sun nemi Shugaban Kasa da Majalisar Kasa da duk masu ruwa da tsaki da su sanya baki cikin lamarin don ganin an yi wa tufkar hanci.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar Sojin Sama Air commodore Edward Gabkwet, ya ce zai bincika tare da sanar da manema labarai halin da ake ciki. Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai tuntube mu ba.