✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata za su koma bakin aiki ranar Litinin – Gwamnati

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa a ranar Laraba za a bude ofisoshin gwamnati a fadin kasar inda wasu ma’aikata za su koma bakin aikinsu…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa a ranar Laraba za a bude ofisoshin gwamnati a fadin kasar inda wasu ma’aikata za su koma bakin aikinsu a ranar Litinin mai zuwa.

Shugaban tsare-tsare na kwamitin yaki da cutar coronavirus Dokta Sani Aliyu, ne ya bayyana hakan lokacin da kwamitin ke gabatar da jawabinsa karo na 22 tun da aka kaddamar da Kwamitin saboda aikin dakile yaduwar cutar.

Aliyu, ya bayyana cewa za a takaita yawan ma’aikatan da za su rika zuwa ofisoshi inda ya jaddada cewa bankuna, kamfanonin gine-gine, masana’antu da ma kamfanonin samar da abinci za su koma a bakin aiki a ranar Litinin din.

Ya ce, bankuna za su bude daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana a kowane wuni tare da tabbatar da an rage yawan masu shiga bankunan kamar yadda gwamnati ta gindaya.

“Za a karfafa gwajin zafin jiki, tsaftar hanyoyin nunfashi da dakatar da duk tarurrukan da ya wuce mutum 20 kuma kwamitin zai ci gaba da ganawa da masu fada aji saboda ganin an samu yanayi na bai daya.

“A ofisoshin gwamnati, ma’aikatan za su koma a ranar 4 ga watan Mayu, amma za a takaita yawansu saboda rage cunkoso a ma’aikatun kuma zamu tattauna da gwamnatocin jihohi don ganin mun samu yanayi na bai daya don fuskantar lamarin.”

“Bankuna za su bude amma za a tsaurara matakai kuma za a rage lokutan aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana tare da hanyoyin kariya da aka umurta ayi amfani dasu.”

“Kamfanoni da suke taka rawa akan samar da abinci za su koma bakin aikinsu. Kamfanonin gine-gine musamman na hanyoyi masu matukar muhimmanci za su koma bakin aikinsu.”

“Masana’antu da kuma kamfanonin samar da magunguna zasu koma aiki tare da rage yawan ma’aikata daga 30 zuwa kashi 50 saboda tabbatar da an bada tazara tsakanin jama’a inda kuma shagunan siyar da magunguna za su kasance a bude dare da rana.”

Dokta Aliyu, ya kara da cewa kasuwanni zasu bude amma makarantu da gidajen siyarda abinci za su kasance a rufe.

“Gidajen siyar da abinci za su kasance a rufe amma za a basu damar kai abinci ga masu bukata zuwa gidajensu. Makarantu zasu kasance a rufe har sai an sake duba lamarin” inji shi.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya sanar da janye dokar hana fita da ya kakaba a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu. An sanya dokar ne tun ranar 29 ga watan Maris saboda dakile yaduwar cutar ta coronavirus a kasar.

A wani jawabi da ya yiwa ‘yan kasar Shugaba Buhari ya amince janye dokar a hankali.