Dandazon ma’aikata karkashin Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) sun yi dafifi a Majalisar Tarayya inda suke zanga-zanga kan yunkurin cire mafi karancin albashi zuwa hannun gwamnoni.
Daruruwan ma’aikatan sun mamaye Majalisar ce don nuna adawarsu ga shirin cire mafi karancin albashi daga cikin jerin kebantattun abubuwa zuwa na yau da kulllum da Majalisar ke yi.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 25 a wani turnuku
- An sa dokar kayyade zancen samari da ’yan mata a Kano
- Yadda ’yan bindiga suka yi garkuwa da masu hakar ma’adinai 100 a Zamfara
Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga Sakatariyar Tarayya zuwa Majalisar Tarayy, suna rera wakokin gwagwarmaya kan kudirin, wanda dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna, Hon. Abbas Tajudeen El-Rufai ya gabatar.
A jawabinsa ga dandazaon masu zanga-zangar, Shugaban NLC na Kasa, Ayuba Wabba, ya ce kudurin bai samu goyon bayan ma’aikatan Najeriya ba, don haka a janye shi nan take ko kuma Majalisar ta gamu da fushinsu.
Ya ce gazawar shugabannin Majalisar Tarayya janye kudirin zai jawo fushin ’yan Najeriya kuma kungiyar kwadago za ta shiga yajin aiki na kasa.
Sai dai Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Alhassan Ado Doguwa da Mataimakin Mai Tsawatarwar Majalisar Dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi sun yi jawabi tare da tabbatar wa masu zanga-zangar cewa Majalisar ba za ta yi wata doka da za ta cutar da ma’aikatan Najeriya ba.
Kungiyar kwadago da sauran kungiyoyin da ke karkashinta a fadin Najeriya na gudanar da zanga-zanga kan batun na mafi karancin albashi.