Wata ma’aikaciyar kamfanin Google ta ajiye aikinta saboda yadda ta yi zargin kamfanin da rufe muryoyin Falasdinawa da rashin yi musu adalci.
Ma’aikaciyar mai suna Ariel Koren ta dauki matakin ne kuma don nuna adawarta da kwangilar lelen asiri ta Dalar Amurka biliyan da miliyan 200 tsakanin Google da Amazon da sojojin Isra’ila.
- An tsare tsohon Ministan Equatorial Guinea saboda sukar Shugaban Kasar
- Buhari ya nada wan matarsa shugabancin kamfanin buga kudi na Najeriya
Ma’aikaciyar ta Google wacce ta zama babbar mai adawa da kwangilar leken asiri da sa ido ta ce sam kamfanin na Google ba ya yi wa Falasdinawan adalci.
Ariel Koren, wacce take rike da mukamin Manajar Tallace-tallace, za ta bar kamfanin a wannan makon, saboda abin da ta ce ya haifar da yanayin aiki mara ban sha’awa ga wasu jama’a da suke son kawo sauyi.
“Zan bar kamfanin Google a wannan makon saboda ramuwar gayya da adawa da ma’aikatan da suka yi magana,” in ji Koren, kamar yadda ta wallafa a shafin Twitter.
“Google ya matsar da aikina zuwa ketare nan da nan bayan na yi adawa da kwangilar sa ido kan kudi $1bn da Isra’ila.”
Rikicin ya fara ne lokacin da Koren ta nuna rashin amincewa da hadin gwiwar bangarorin guda uku a kan wani shiri mai suna Project Nimbus.
Ta shafe fiye da shekara guda tana shirya adawar don shawo kan Google ya janye daga yarjejeniyar, ciki har da zagayawa da korafe-korafe na masu fafutuka da kuma yin magana da shugabannin kamfanin da yin magana da kungiyoyin labarai.
Duk da haka, Koren ta ce maimakon sauraron damuwarta, Google ya yi watsi da bukatarta a watan Nuwamban 2021 tare da wa’adin: ko dai ta yarda ta tashi daga San Francisco a Jihar California ta Amurka zuwa Sao Paulo a kasar Brazil ko kuma ta rasa aikinta.
Koren ta ce babu wata hujja ta kasuwanci game da matakin da aka umarce ta kuma ta shigar da kara ga Hukumar Kula da Huldar Kwadago ta Kasar (NLRB).