✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikacin banki ya yi kisa a wurin karbo bashi

Wani jami'in banki ya kashe matar wani kwastoma a lokacin da ma'aikatan bankin suka je gidan mutumin karbo bashin da bankin ya ba shi.

Wani ma’aikacin banki ya kashe matar wani kwastoma da suka yi wa takakkiya har gida domin karbo bashin da bankinsu ya ba shi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta ce ta cafke jami’an bankin su hudu da suka je gidan, kan zargin mutuwar matar auren mai suna Misis Vivian Omo.

Aminiya ta gano cewa mijin matar ya karbi bashi ne daga wani bankin raya kananan masana’antu da ke  Abule Ijoko, a yankin Lemode da ke Karamar Hukumar Ifo ta jihar, amma bai biya ba.

A kan haka ne ma’aikatan bankin suka yi takakkiya zuwa gidansa da nufin karbo kudin, amma matar tasa mai shekara 50 ta shaida musu cewa ba ya nan.

Amma da ba su gamsu ba, sai suka kutsa cikin gidan suka fara kwashe kayayyakin laturoni, amma matar tasa ta yi yunkurin hana su.

Kakakin ’yan sandan jihar ta Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce, “A yayin da take kokawar hana ma’aikatan tafiya da kayan ne daya daga cikinsu ya ture ta, ta fadi magashiyyan.

“Ko da aka garzaya da ita zuwa asibiti, sai likitoci suka sanar cewa rai ya riga ya yi halinsa.”

A cewarsa, an ajiye gawar a Babban Asibitin Ido, domin gudanar da bincike.

Ya ce bayyana cewa na cafke jami’an bankin ne a ranar Laraba bayan ’yar matar ta kai kara a babban caji ofis na yankin Alagbado.

Oyeyemi ya gargadi ma’aikatan cibiyoyin hadahadar kudi da su rika bin doka wajen karbo bashin da suka bayar, su guji daukar doka a hannunsu, domin duk wanda rundunar ta kama zai fuskanci hukunci.