✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lyon ta dakatar da dan wasanta saboda tsananin banka tusa

Dan wasan ya yi fice wajen banka tusa, lamarin da ya fusata da dama a kungiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta dakatar da dan wasan bayanta, Marcelo saboda dabi’arsa ta tsananin banka tusa ga sauran ’yan wasan kungiyar.

Wannan ya biyo bayan yawan sakin tusar da Marcelo ya dinga yi yana kuma dariya a cikin dakin shiryawar ’yan wasan kungiyar bayan sun sha kashi a hannun Angers da ci 3 – 1.

Tuni hukumar gudanarwar Lyon ta fitar da sanarwa kan halayyar dan wasan, tare da tsattsauran kashedi ga sauran ’yan wasanta kan mummunar dabi’ar.

Har wa yau, kungiyar ta mayar da Marcelo tawagar ’yan wasanta gajiyayyu, inda a nan zai ci gaba da murza leda a halin yanzu.

Ta kuma sanar da cire dan wasan mai shekara 34 daga ’yan wasanta da za su ke buga mata wasanni tun bayan faruwar lamarin.