✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lukaku ba ya karbar kyauta daga kamfanin giya

Rahotanni sun nuna dan kwallon gaba a kulob din Manchester United na Ingila Romelu Lukaku yana daga cikin ’yan kwallon da ba sa karbar duk…

Rahotanni sun nuna dan kwallon gaba a kulob din Manchester United na Ingila Romelu Lukaku yana daga cikin ’yan kwallon da ba sa karbar duk wata kyauta da ta fito daga wani kamfanin giya komai darajarta.

Lukaku dan asalin Beljiyum, cikakken Musulmi wanda kulob din Manchester United ya saye shi daga kulob din Eberton a watan jiya a kan Fam Miliyan  75 yana daga cikin ’yan kwallo 21 da Kamfanin  yin giya na Heineken mai daukar nauyin Gasar Zakarun Kuloba na Turai (Champions League) ya ware sunayensu a matsayin wadanda ko ya ba su kyauta ba sa karba saboda biyayyarsu ga addinin Musulunci. 

Kamfanin yin giya na Heineken ne yake daukar nauyin gasar sada zumunta da yanzu haka take gudana a Amurka (ICC Cup), kuma Lukaku ne dan kwallo mafi kwazo a wasan da Manchester United ta yi da na Manchester City a makon jiya, kuma shi ya zura kwallo daya daga cikin kwallayen biyun da United din ta zura a ragar City a wasan.

Rashin karbar kyautar ta sa kanfanin Heineken ya mika ta ga daya daga cikin ’yan kwallon Manchester Henrikh Mkhitaryan a maimakon Lukaku.