Dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid Luka Modric ya tafi Saudiya don tattaunawa da kungiyar Al-Nassr inda tsohon abokin wasansa Cristiano Ronaldo yake.
Wannan na zuwa ne gabanin yunkurin da ake na ganin dan wasan ya koma buga wasa a gasar Saudi Pro League.
- Jihohi 12 da Abuja da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet
- An zaɓi Musulmi shugaban gwamnatin Scotland
Kungiyar ta Al-Nassr na shirin dauko dan wasan na Croatia, wanda ya koma Real Madrid daga Tottenham kan kudi Euro miliyan 35 a shekarar 2012.
Tun bayan komawarsa Madrid, dan wasan ya samu nasarar lashe kofuna 22 a kungiyar da kuma kyautar Ballon d’Or.