✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Luis Castro zai koma horar da ’yan wasan Al-Nassr

Castro zai rattaba hannu a kwantiragin shekaru biyu da Al-Nassr.

Kocin nan dan kasar Portugal, Luis Castro zai bar kungiyar Botafogo ta Brazil zuwa Al-Nassr ta kasar Saudiya, inda zai hade da dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo.

Castro, mai shekaru 61, ya amince ya karbi wannan aiki mai gwabi na horar da Al Nassr, wadda Cristiano Ronaldo ne kyaftin din ta.

Al-Nassr ta nemi sabon koci ne sakamakon sallamar kocinta, Rudi Garcia da ta yi a watan Afrilu.

Ronaldo ne da kansa ya tuntubi Castro, kuma ya shawo kansa har ya amince ya karbi wannan aiki daga Al-Nassr, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

Wasan rukuni na gasar cin kofin kungiyoyin kasashen Kudancin Amurka, wato Copa Sudamericana na jiya Alhamis ne wasan Castro na karshe a matsayin kocin Botafago.

Castro zai rattaba hannu a kwantiragin shekaru biyu da Al-Nassr, kuma akwai zabin tsawaitawa nan gaba.