A makon jiya ne dai, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Gida Mustapha ya kaddamar da kwamitin mutum 14 a kan tsarin samar da ‘yan sanda daga al’umma. Kwamitin wanda DDokta Amina Shamaki, Babbar Sakatariya a Gwamnatin Tarayya ke shugabanta, an dora masa nauyin nazartar sakamakon wani nazari a kan halin tabarbarewar tsaro da Cibiyar Tsare-tsare da Horar da Dabarun Mulki ta Kasa ta gudanar, mai taken “Rahoton Musayar Yawu na Fadar Shugaban Kasa.”
Da yake rantsar da kwamitin, Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya yi bitar ire-iren ababuwan da ya ce su ke haddasa rashin tsaro a Najeriya da suka hada da rashin kyawun hadakar tsare-tsare da maimai tare kuma da rashin aiwatar da tsaren-tsaren yadda ya kamata da ta’allaka ikon aikin ‘yan sanda a matakin tsakiya (Gwamnatin Tarayya) da ma kuma rauni ta fuskar sa ido da bitar ayyukan tsare-tsaren tsaron. Sakataren ya kara da lissafta sauran kalubalen da cewa, akwai rashin aiki da fasaha tare da sabbin ababuwa na zamani da rashin kundin bayanan ‘yan kasa na bai daya da zai taimaka wajen gudanar da tsaron cikin gida. Akwai kuma rashin samar da kasafin kudin da ya dace ga sha’anin tsaro, sai kuma rashin yarda da aminta ga kafofi ko kuma rundunonin tsaron kasar.
Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya nuna cewa, a sakamakon tabarbarewan halin tsaro a Najeriyar, ya kai ga a yanzu ‘yan kasar na kiran da a dawo da ‘yan sandan jihohi. Ya ce tun zuwan gwamnatin nan da kuma dukkan irin kudaden da aka kashe don tsaro tare da nasarorin da aka samar ta fuskar tsaron, hakan bai taka wa wadannan kiraye-kirayen birki ba.
Gwamnatin ta yi abin da ya kamata wajen kafa wannan kwamitin. Sanannen abu ne yadda ake zaman doya da manja tare da samun gibi tsakanin rundunar ‘yan sandan kasar da kuma al’ummomin Najeriya. Kamar dai yadda Sakataren ya nuna, hakan bai rasa nasaba da irin rashin amintar ‘yan kasar da jami’an ‘yan sanda wajen tsegunta musu bayanan sirri a kan aikace-aikace da ma maboyar masu aikata miyagun laifuka. Kasancewar, masu aikata laifukkan na zama ne a cikin jama’a, kuma su jama’ar sun san su. Babban misalin yadda ‘yan sandan cikin al’umma ya yi nasarar taimakawa tsaro, shi ne a Jihar Borno, inda samar da Samari ‘Yan Gora da aka fi sani da Cibilian JTF ya matukar kawo sauyi a dabarun yakin da kasar ke yi da ayyukan ta’addanci. Wadannan matasan sun yi wa ‘yan Boko Haram farin sani kuma sun taimaka wa sojoji wajen kamewa tare da fatattakar ‘yan kungiyar daga cikin birnin Maiduguri.
Bugu da kari, a dai kan wannan matsalar, shugabannin gargajiya na samun bayanan sirri game da masu aikata laifuka cikin yankunansu. Sukan fada wa Dagatai da Hakimai da kungiyoyin matasa da ma shugabannin kungiyoyin addinai da su tattara bayanan duk wani bara-gurbi da ke zama cikinsu. Akwai bukatar ‘yan sanda su yi aiki kafada da kafada da shugabannin gargajiya, muddin dai a shirye suke su dakile aikata laifuka. Sau tarin yawa, wadannan shugabannin gargajiyar kan zama ba su da ikon komai ko da kuwa suna sane da bara-gurbi cikinsu, sakamakon yadda rashin yadda da suka yi da jami’an ‘yan sandan wajen tsegunta musu bayanan sirrin.
Muna kira ga kwamitin da ya yi aikin da ya dace ta hanyar zakulo kyawawan manufofi da ma matakan da ‘yan sandan za su bi don samun yarda da kuma amintar al’umma. ‘Yan sandan ba za su taba samun nasarar ragewa ko kawar da miyagun ayyuka a kasar nan ba, har sai sun samu hadin kan al’ummomi daban-daban. Sakamakon gazawar ‘yan sandan wajen dakile aikata laifuka, hakan ya haifar da bayyanar kungiyoyin ‘yan banga a kusan dukkan kusuruwowin kasar da zimmar maye aikin ‘yan sandan, sai dai akasarinsu ba su gudanar da aikin bisa ka’ida. Kai wasu al’ummomin ma, kusan sun rungumi daukar matakin kare kansu da kansu, inda suke daukar doka a hannunsu, har ya kai ga sukan yi kisa ba bisa doron shari’a ba, kawai saboda rashin yadda da tsarin shari’a da na jami’an tsaro. Wannan abin kaico ne matuka kuma lallai ne a yi duk mai yiwuwa a dakatar da hakan.
Zancen gaskiya, a halin yanzu a Najeriya, tsarin tsaron kasar bai yi wani tanadin samar wa ‘yan kasar tsaro ba, musamman wadanda ke zama a yankunan karkara, wuraren da da wuya ma za ka samu jami’an ‘yan sanda a can. A shawarwarin da za su bayar, ya kamata kwamitin ya zayyana karara, matakan da za a bi wajen kare al’ummomin karkara da miyagun ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashi, wadanda suke cin karensu babu babbaka. Dole ne a yi duba na tsanaki a kan dukkanin zabin da ake da shi a kasa da ya hada da inganta aiki da fasahar tsaro na zamani da ma samar da ‘yan sandan jiha.