✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lois Auta: Ba nakasasshe sai kasasshe

Lois Auta jajirtacciya ce wajen neman na-kai da kare hakkin nakasassu

Lois Auta na fuskantar kalubale biyu wadanda kan yi tarnaki ga mai son taka rawa a al’umma: ga ta mace, sannan kuma mai bukata ta musamman.

Tun tana karama cutar Polio, wato Shan-Inna, ta shanye mata kafafu, don haka sai a keken guragu take kai-kawo.

Amma kuma ba ta bari kowanne daga cikin kalubalan biyu ya dankwafar da ita ba, balle ta zauna tana “Allah ba ku mu samu”.

Ba kawai tashi tsaye Lois Auta ta yi don ta cim ma burinta a rayuwa ba, har ma fafutuka take yi don kwato wa masu yanayi irin nata hakkokinsu da taimaka musu su kai ga biyan nasu bukatun.

Don haka ne ma ta kafa gidauniyar Cedar Seed Foundation mai tallafa wa nakasassu don su yi karatu su yi sana’a.

Masu sha’awar siyasa ma ana karfafa musu gwiwa sannan ana koyar da su dabaru irin na siyasa.

Gwagwarmayar siyasa

Ita kanta ta taba tsayawa takara tana neman kujera a Majalisar Wakilai ta Najeriya amma baya ga kalubalen da take fuskanta wani kalubalen na uku – kabilanci – ya yi mata tarnaki.

Duk da haka ba ta karaya ba, ta sha alwashin komawa jiharta ta asali don sake tsayawa.

Ganin kokarin Lois Auta ne ya sa mata masu bukata ta musamman suka zabe ta a matsayin Shugabar Kungiyar Mata Nakasassu.

Bayan haka, tana taka rawa a matakin shugabanci a kungiyoyin nakasassu daban-daban irin su Kungiyar Mata Guragu (Women on Wheels) da Kungiyar Nakasassu Masu Shugabancin Al’umma.

Lambobin yabo

Tauraruwar tamu ta samu lambobin yabo da dama, ta kuma samu shiga a wasu shirye-shirye na musamman na ilimi ko tsara manufa ko wani abu mai kama da haka.

Taron Tattalin Arziki na Duniya ya taba nada ta Matashiyar Jagora a Duniya, sannan tana cikin shirin Matasan Jagororin Afirka na Mandela Washington.

Bugu da kari, Tauraruwar tamu ta yi kwas na Ashoka don mutanen da ke da wata basira ta musamman da za ta iya inganta rayuwar al’umma.

Ayyuka na musamman

Lois Auta na cikin mutanen da suka tsara wa Najeriya makoma zuwa shekara ta 2020, wato Vision 20:2020, ta fuskar tattalin arziki.

A yanzu haka kuma mamba ce ta Agenda 2050, wani kwamiti da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar don ya tsara yadda za a raba ’yan Najeriya miliyan 100 da talauci a shekara 10 masu zuwa.

Haka kuma tana cikin kwamitin da ke bai wa Ministar Mata shawara a kan al’amuran da suka shafi ’yan kasuwa.